Yan Bindiga Sun Nemi a Basu Miliyan N10m Kafin Su Saki Malamin Jami'ar UNIJOS, ASUU

Yan Bindiga Sun Nemi a Basu Miliyan N10m Kafin Su Saki Malamin Jami'ar UNIJOS, ASUU

Yan bindigan sa duka sace malamin jami'ar Jos (UNIJOS) sun nemi a basu miliyan N10m a matsayin kuɗin fansa kafin su sake shi, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Mgana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

Dr Lazarus Maigoro, shugaban ƙungiyar ASSU reshen UNIJOS, shine ya tabbatar da haka da hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN).

Yan Bindiga Sun Nemi a Basu Miliyan N10m Kafin Su Saki Malamin Jami'ar UNIJOS, ASUU
Yan Bindiga Sun Nemi a Basu Miliyan N10m Kafin Su Saki Malamin Jami'ar UNIJOS, ASUU Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu yan bindiga sun kutsa har cikin gidan, Dr Dan Ella, dake yankin gidajen 'Haske Quaters' a garin Lamingo, ƙaramar hukumar Jos ta arewa, inda suka yi awon gaba da shi.

KARANTA ANAN: Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka

"Wannan abu ne mara daɗi ace yan bindiga na bibiyar mambobin mu, a yanzu da nike maganan nan da ku sun nemi a basu miliyan N10m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako shi." inji shugaban ASUU-UNIJOS.

Shugaban ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su yi duk me yuwuwa domin su kuɓutar da ɗan uwansu dake hannu yan ta'adda.

Hakanan ya roƙi jami'an da su ƙara zage dantse wajen kawo ƙarshen dukkan ƙalubalen tsaron da kasar nan ke fama da shi.

A wani labarin kuma kuma Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai

Wata ɗaliba dake ajin ƙarshe a jami'ar BUK Kano ta rigamu gidan gaskiya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ɗalibar mai suna, Mercy Sunday, ta mutu ne a safiyar ranar Talata kamar yadda ƙawarta ta faɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262