'Yan sanda sun cafke mutum 15 da ke zargin ƴan ƙungiyar asiri ne

'Yan sanda sun cafke mutum 15 da ke zargin ƴan ƙungiyar asiri ne

  • Yan sanda a ƙaramar hukumar Eket jihar Akwa Ibom sun ce sun kama mutum 15 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne
  • Mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar ya ce an kai sumame wani wani matattarar ɓata gari aka kamo su
  • Shugaban ƙaramar hukumar Eket, Akaninyene Tommy ya kuma ce an rufe wasu otel biyu a ƙaramar hukumar ta aka tabbatar nan ɓata gari ke taruwa suna aikata laifuka

Rundunar yan sandan Nigeria a jihar Akwa Ibom ta ce ta kama mutum 15 da ake zargin ƴan ƙungiyoyin asiri ne a ƙaramar hukumar Eket, PM News ta ruwaito.

Today NG ta ruwaito mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Odiko Macdon, ne ya sanar da hakan a yayin hirar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a.

Jami'an Yan Sandan Nigeria
Jami'an Yan Sandan Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Ya ce jam'ian rundunar su kai samame wani fitaccen matattarar ɓatagari da ke Afaha Ukwu a ƙaramar hukumar suka kama su.

A cewar rahotanni, kungiyoyin asirin biyu sun soma sabuwar rikici ne a ranar 21 g watan Yuni kuma kawo yanzu mutum 3 sun mutu a Eket.

Kakakin yan sandan ya ce, "Mun kama mutum 15 da muke zargin ƴan ƙungiyar asiri ne yayin samamen da muka kai a maɓuyar ɓatagari a Eket da kewaye. Idan ka yi samame ka kama mutum 15, hakan baya nufin dukkansu masu laifi ne."

Mr Macdon ya yi bayanin cewa kwamishinan ƴan sanda ya bada umurnin a tantance su a gurfanar da wadanda aka samu da laifi a kotu.

KU KARANTA: Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

Ya kara da cewa rundunar za ta cigaba da kai samame wuraren da aka san ɓata gari na taruwa a Eket da kewaye.

An rufe otel biyu da ɓata gari ke zama

A bangarensa, shugaban ƙaramar hukumar Eket, Mr Akaninyene Tommy ya rufe otel biyu a Afaha Uqua da Ofriyo inda masu laifin ke ɓuya suna laifinsu.

"An rufe otel din an kuma ce su dakatar da ayyukansu har sai Baba ta gani, duk lokacin da ake rikici a Eket, daga Otel abin ke tasowa.
"A matsayin mu na gwamnati, za mu tabbatar cewa ba a sake bude wuraren ba don yin aiki, " a cewar Tommy.

Ya yabawa yan sandan bisa aikin da suka yi yana mai cewa kada su raga wa duk wani mai laifi domin tabbatar da tsaro a Eket ne abin da ya fi muhimmanci a wurinsa.

A wani labarin daban, wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an ajiye wani kambun tsafi a gaban babban ofishin yan sanda na jihar Abia.

An gano cewa mazauna Bende road a Umuahia, babban birnin jihar, a ranar Talata 22 ga watan Yuni sun farka sun ga an ajiye abin tsafin a inda aka takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel