An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

  • Wani abin tsafi da aka gani a gaban ofishin yan sandan jihar Abia ya dauki hankulan yan Nigeria
  • A cewar rahotanni da ke shigiowa, an ajiye kambun tsafin ne a kusa da Bende roada a Umuahia, babban birnin jihar don fatattakar yan bindiga
  • SP Geoffrey Ogbonna, mai magana da yawun yan sandan jihar bai yi tsokaci kan lamarin ba kawo yanzu

Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an ajiye wani kambun tsafi a gaban babban ofishin yan sanda na jihar Abia.

An gano cewa mazauna Bende road a Umuahia, babban birnin jihar, a ranar Talata 22 ga watan Yuni sun farka sun ga an ajiye abin tsafin a inda aka takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa.

Mazauna Abia sun farka sun ga abin tsafi a gaban ofishin yan sanda
Mazauna Abia sun farka sun ga abin tsafi a gaban ofishin yan sanda. Hoto: Daily Trust
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

Duk da cewa a yanzu Legit.ng bata samu damar tabbatar da ikirarin ba, rahoton da jaridar ta wallafa ya ambaci cewa mazauna unguwar sunyi ikirarin cewa an ajiye kambun tsafin ne don kare jami'an tsaro daga yan bindiga.

Amma, mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna kawo yanzu bai ce komai game da lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.

Yan bindiga na cigaba da kaiwa jami'an tsaro hari a yankin kudu, jami'an tsaron na ta rasa rayyukansu.

KU KARANTA: 'Barayi sunyi hatsari cikin motar da suka sace, ɗaya ya mutu biyu sun jikkata

Yan daba sun kona ofishin yan sanda na jihar Abia

Harin na zuwa ne wata daya bayan yan bindiga sun tada hankulan mutanen karamar hukumar Bende bayan kai hari unguwar yan sanda ta Ubani Market tare da kona shi.

Rahotanni sun ce ba a rasa rai ba sakamakon harin da aka kai a ranar Lahadi 9 ga watan Mayu sai dai hakan ya tilastawa yan sanda da ke caji ofis din komawa wani unguwa da ke kusa da su mai suna Trade-Moore housing estate.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel