Wata makaranta a Kano ta amince iyaye su riƙa biyan kuɗin makaranta da 'cryptocurrency'

Wata makaranta a Kano ta amince iyaye su riƙa biyan kuɗin makaranta da 'cryptocurrency'

  • Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano, New Oxford Science Academy, ta fara karbar kudin makaranta da cryptocurrency
  • Sabi'u Musa Haruna, shugaban makarantar ya tabbatarwa manema labarai hakan a ranar Alhamis yana mai cewa sun tuntubi iyaye kafin daukan matakin
  • Musa Haruna ya bada misalin makarantun kasashen waje da suke karbar kudin crypto din da ya ce zamani ne ya zo dashi kuma ya yi imanin nan gaba kowa zai rungumi abin

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano mai suna New Oxford Science Academy, Chiranci, ta ce tana karbar kudin crypto a matsayin kudin makaranta.

Shugaban makarantar, Sabi'u Musa Haruna, ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Tambarin kudaden zamani na cryptocurrency
Tambarin kudaden zamani na cryptocurrency. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya lallasa abokan hammayarsa ya zama dan takarar gwamnan APGA

A cewarsa, an amince da hakan ne bayan mahukunta a makarantar sun tattauna da iyayen dalibai.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Haruna ya kara da cewa an dauki matakin ne da nufin saukaka wa iyaye biyan kudin makaranta.

Ya ce:

"Mun amince za su rika karbar kudin crypto wurin biyan kudin makaranta saboda duniya ta fara karkata zuwa wannan tsarin.
"Mun yi imanin cewa wata rana duniya za ta fi amincewa da kudin crypto fiye da kudin takarda."

KU KARANTA: 2023: Yadda za ka yi rajistan katin zaɓe a shafin INEC da wayar salula cikin sauƙi

Mr Haruna ya kara da cewa kasashe kamar El-Salvador da Tanzania tuni sun fara karbar kudin crypto a makarantunsu.

Don haka, ya bukaci gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi gaggawar rungumar tsarin ta kuma saka dokoki domin yin amfani da shi.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel