Da Duminsa: Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya lallasa abokan hammayarsa ya zama dan takarar gwamnan APGA

Da Duminsa: Tsohon gwamnan babban bankin Nigeria ya lallasa abokan hammayarsa ya zama dan takarar gwamnan APGA

  • Charlesa Soludo ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar APGA a zaben da ke tafe a jihar Anambra
  • Hakan ya biyo bayan nasarar da tsohon gwamnan na CBN ya samu ne a zaben fidda gwani na jam'iyyar
  • Soludu ya lashe zaben duk da dakatarwar da wani tsagi na jam'iyyar APGA wacce ke mulki a jihar ta yi masa

Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA.

A cewar Daily Trust, Soludo ya samu kuri'u 740 inda ya doke Ezenwanko Christopher da ya samu kuri'u 41, ThankGod Ibe da ya samu kuri'u 4 da Okolo Chibuzor wanda ya samu kuri'u bakwai.

Charles Soludo ya zama dan takarar jam'iyyar APGA gabanin zaben 6 ga watan Nuwamba a Anambra.
Charles Soludo ya zama dan takarar jam'iyyar APGA gabanin zaben 6 ga watan Nuwamba a Anambra. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

The Cable ta ruwaito cewa jimillar kuri'un da aka tantance wanda wakilai za su kada 795 ne yayin da kuri'u 792 ne aka kada yayin zaben.

Bayan nasarar da ya samu, Soludo zai wakilci jam'iyyar ta APGA a zaben gwamna da ake shirin yi a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamban 2021.

Tawagar jam'iyyar APGA na kasa karkashin jagorancin Sampson Segun Olalaye ne suka jagoranci yin zaben.

Bayan nasarar da ya samu, Soludo ya jinjinawa wakilan bisa zabensa da suka yi.

An yi zaben fidda gwanin ne a ranar Laraba 23 ga watan Yuni a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Gwamnan jihar Willie Obiano da wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun hallarci wurin zaben.

KU KARANTA: Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan kwankwaɗar wani maganin gargajiya

Abin da Gwamna Obiano ya ce game da nasarar Soludo

Gwamna Willie Obiano ya taya dan takarar bisa nasarar da ya samu a zaben kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce nasarar Solodo ya nuna cewa har yanzu jamiyyar tana nan tsintsiya madaurinki daya, yana mai bata tabbacin cewa APGA ne za ta lashe zaben gwamna da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Tsagin Jude Okeke

Bangaren Jude Okeke na jam'iyyar ta APGA za ta yi zaben fidda gwaninta a ranar 1 ga watan Yulin 2020.

Tunda farko tsagin na Okeke ta dakatar da tsohon gwamnan na CBN.

A wani labarin daban, kun ji cewa Alhaji Bello Dankande, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, ya rasu yana da shekaru 56 a duniya, PM News ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa Alhaji Lawan Liman, shugaban jam'iyyar APC na riko a jihar, ne ya sanar da rasuwar yayin hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Talata a Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Online view pixel