2023: Yadda za ka yi rajistan katin zaɓe a shafin INEC da wayar salula cikin sauƙi

2023: Yadda za ka yi rajistan katin zaɓe a shafin INEC da wayar salula cikin sauƙi

  • An zamanantar da yin rajistan katin zabe ta hanyar bude shafin yanar gizo inda mutane za su iya yin rajista
  • An sa ran yan Nigeria da suka cika ka'idojin zabe za su tafi shafin su cike bayanai da ake bukata kafin su tafi cibiyoyin rajista su karasa
  • Za a bude shafin ne daga ranar Litinin 28 ga watan Yunin shekarar 2021, a lokacin da ake sa ran fara yin rajistar

Gabanin babban zaben kasa na shekarar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ta kaddamar ta shafin yanar gizo inda yan Nigeria za su rika yin rajistan katin zabe.

Wani takaitaccen bayani da aka wallafa a shafin Facebook na hukumar ta INEC ya nuna cewa shafin da za a iya ziyarta a http://www.cvr.inecnigeria.org/ zai fara aiki ne a ranar Litinin 28 ga watan Yuni, kuma a ranar za a fara rajitsan.

2023: INEC ta kaddamar da sabon shafin yin rajistan katin zabe ta yanar gizo
2023: INEC ta kaddamar da sabon shafin yin rajistan katin zabe ta yanar gizo. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC na ksa ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa an kaddamar da shafin ne domin masu son yin rajistan su fara yin rajistan, sannan su zabi ranar da za su tafi cibiyoyin rajistan domin a karasa musu, The Cable ta ruwaito hakan.

Legit.ng ta gano cewa masu son yin rasjistan za su iya zuwa ofishin INEC a jiha ko karamar hukuma su karasa yin rajistan daga ranar Litinin 19 ga watan Yuli da aka sa ran fara karasa rajistan a ofisoshin INEC.

Katin zabe na INEC: Yadda za a yi rajista a saukake

1. Masu son rajistan su ziyarci https://cvr.inec.gov.ng or https://cvr.inecnigeria.org a na'urar da suke shiga yanar gizo don fara rajistan.

2. Mai son rajistan ya fara bude asusu da shafin ta hanyar amfani da adireshin imel domin fara rajistan.

3. Bayan bude asusun, za a tura maka sako cikin imel din da ka yi rajista da shi.

4. Ka bude imel din ka, ka latsa sakon don tabbatarwa sannan ka cigaba da rajistan

5. Mai yin rajistan zai cike bayanansa a shafin da ya bude.

6. Bayan cike bayanan cikin fom, sai ka zabi rana da cibiyar rajista da kake son zuwa domin a karasa maka rajistan a kuma dauki hotonka da na zanen yatsu.

KU KARANTA: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

7. Mai rajistan zai latsa 'submit' bayan an karasa maka rajistan, daga nan za ka fitar da takarda mai dauke da bayanan ka.

8. Sai ka yi printing din takardar mai dauke da bayanan ka.

9. Ka ziyarci cibiyar rajista na INEC da takardar ka a ranar da ka zaba domin a dauki bayanan ka.

10. Za a baka takardar shaidar cewa ka kammala rajistar wadda za ka yi amfani da shi ka karba katin zaben idan ya fito.

Yin rajistan a shafin yanar gizo kyauta ne

A cewar INEC, yin rajistan a shafin ta na yanar gizo kyauta ne. Abin da ake bukata kawai shine wayar salula ko kwamfuta ko wata na'ura da ake iya shiga yanar gizo da ita.

Farfesa Mahmood ya kara da cewa INEC ta siyo dukkan kayayakin da ake bukata domin yi wa masu zaben rajitsa kuma za ta tura ma'aikata 5,346 zuwa cibiyoyin rajista.

A wani labarin daban, Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA.

A cewar Daily Trust, Soludo ya samu kuri'u 740 inda ya doke Ezenwanko Christopher da ya samu kuri'u 41, ThankGod Ibe da ya samu kuri'u 4 da Okolo Chibuzor wanda ya samu kuri'u bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel