Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

  • Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Bello Dankande ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayi Bello Dankande ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Gusau bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Shugaban riko na jam'iyyar APC a Zamfara, Lawan Liman ya tabbatar da rasuwar ya kuma mika ta'aziyya ga yan jam'iyyar da iyalan mamacin

Alhaji Bello Dankande, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, ya rasu yana da shekaru 56 a duniya, PM News ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa Alhaji Lawan Liman, shugaban jam'iyyar APC na riko a jihar, ne ya sanar da rasuwar yayin hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Talata a Gusau.

Alhaji Bello Dankande
Jigo a APC, Alhaji Bello Dankande. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Liman ya ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Gusau bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, a ranar Talata.

Ya ce:

"A madadin daukakin 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar, ina mika sakon ta'aziyya ga jagoran APC a jihar, Alhaji Abdulaziz Yari da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar game da rashin da muka yi.
"Ina addu'ar Allah SubhanahuWata’ala ya saka masa da Aljannatul Firdausi ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa."

KU KARANTA: Bangarori biyu na jam'iyyar APC sun yi rikici, an harbi mutum biyu wasu da dama sun jikkata

Mukaman da ya rike kafin rasuwarsa

Dankande ne tsohon kwamishina na harkokin kananan hukumomi da masarautu a jihar na Zamfara.

Shine dan takarar jam'iyyar APC a zaben da aka yi a Disambar 2020 a zaben sharar fage na kujerar wakilin Bakura a Majalisar dokokin jihar, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bakura.

Ya rasu ya bar matan aure uku, 'ya'ya 20 da jikoki da dama.

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar a siyo mata tsintsiya guda miliyan uku daga masu siyarwa a kasuwanni don sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Calabar.

Mr Ita ya ce an gano kwastam an samu karancin tsintsiya a jihar, wanda shine alama na jam'iyyar, bayan mutane da yawa sunyi tururuwan shiga jam'iyyar bayan gwamnan jihar Ben Ayade ya shigo jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel