A bai wa ’yan bindiga aikin kare dazukanmu domin dorewar zaman lafiya - Sheikh Gumi

A bai wa ’yan bindiga aikin kare dazukanmu domin dorewar zaman lafiya - Sheikh Gumi

  • Sheik Gumi yace su kansu al’ummomin makiyayan ana aikata miyagun laifuka a kansu a sassan kasar nan
  • Ya kwatanta abin da ke faruwa a Najeriya a halin yanzu a zaman yakin kabilanci
  • A cewarsa, ya dace gwamnati ta yi wa makiyayan afuwa kamar yadda aka taba yi wa tsagerun yankin Neja Delta

Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Gumi ya bayyana cewa Najeriya na fama da yaki mai nasaba da kabilanci, yana mai kiran da a yi afuwa ga ’yan bindigar da ke addabar jama’a idan dai har za su bar aikata miyagun laifukan.

Ya bukaci manoma a duk fadin kasar nan da su ba makiyaya damar kare dazuzzukan nasu.

A cewar malamin, lura da yakin kabilanci da ke faruwa a kasar nan lallai ne gwamnatin tarayya kada ta nuna bangaranci ko goyon bayan wani sashe guda.

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

Sheikh Gumi da yan bindiga
A bai wa ’yan bindiga aikin kare dazukanmu domin dorewar zaman lafiya - Sheikh Gumi Hoto: Dr Ahmad Gumi
Asali: UGC

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Babban malamin, koda yake ya amince cewa 'yan bindigar suna aikata kowane nau'in laifi, sai dai ya ce, wadansu kabilun kasar nan sun yi wa al’ummar Fulanin ta’asa kala-kala.

Da yake kafewa kan kiran nasa na yi wa 'yan bindigar afuwa, malamin ya ce a shirye suke su mika wuya idan gwamnati za ta samar musu da ayyukan yi ta yadda za su dogara da kansu.

Gumi a hirar sa da gidan telebijin na Arise a safiyar Laraba yace:

“Dauki misalin yankin Neja Delta, ina ganin za mu iya daukar karatu daga nan. Lokacin da suke lalata bututan mai, an ba su aikin kare bututan man.
“A halin yanzu, makiyayan suke iko da wagegen yanki na dazukanmu inda suke hana manoma noma. Kamar yadda Yankin Neja Delta ke da muhimmanci ga tattalin arziki, haka nan suma wadannan makiyaya suke da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya.
“Za su iya zama masu tsaronmu, za su iya tsaron gandun dazukan kasar nan. Suna da kwarewar da za mu iya amfana da ita."

Sai dai malamin ya yi fatali da afuwar da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yi wa ’yan bindigar inda ya bayyana ta a zaman ‘afuwar siyasa’ wacce ba ta da wani abin toshiyar baki.

Gwamnati na sane da abinda nakeyi

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya ce shiga daji da yake yi domin tattaunawa da 'yan bindiga duk yana yi ne da hadin guiwar hukumomin gwamnati da cibiyoyin tsaro.

Gumi ya tabbatar da cewa bai taba yin wani laifi ba in dai batun shiga daji ne domin tattaunawa da 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel