FG tana sane da alakata da 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya yi bayani

FG tana sane da alakata da 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya yi bayani

  • Gumi wanda ya samu suka daban-daban a cikin kwanakin nan, ya ce gwamnatin tarayya tana sane sarai da alakarsa da 'yan bindiga
  • Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi yayi martani kan rahoton dake yawo na cewa jami'an DSS sun neme shi
  • Malamin mazaunin jihar Kaduna ya musanta zargin da ake masa na cewa yana wasu kalamai marasa dadi game da rundunar soji

Jihar Kaduna

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya ce shiga daji da yake yi domin tattaunawa da 'yan bindiga duk yana yi ne da hadin guiwar hukumomin gwamnati da cibiyoyin tsaro.

Gumi ya tabbatar da cewa bai taba yin wani laifi ba in dai batun shiga daji ne domin tattaunawa da 'yan bindiga, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane

FG tana sane da alakata da 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya yi bayani
FG tana sane da alakata da 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya yi bayani. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango

Ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni bayan kammala sallar Juma'a a masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna.

Gumi ya ce: "Babu wanda ya gayyaceni domin ansa tambayoyi ko kuma kama ni, zan iya tabbatar da hakan."

Shehin malamin ya kara da cewa, "Tunda na fara shiga daji, na je da sanin jami'an tsaro, 'yan sandan farin kaya, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin Fulani. Ban taba zuwa ni kadai ba."

Vanguard ta ruwaito cewa malamin ya musanta kalamai marasa dadi da aka ce yayi kan rundunar soji yayin da aka tattauna da shi kai tsaye a gidan talabijin na kasa.

Ya ce babu inda a tattaunawar ya zargi rundunar sojin. Malamin dan asalin Kaduna ya musanta cewa jami'an tsaron farin kaya na tuhumarsa ne saboda tsokacin da yayi kan rundunar sojin.

A wani labari na daban, shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa'o'i 48.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng