Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

  • Sanata Ahmad Lawan ya ce ba zai yiwu a cigaba da tatsan kudi daga wajen yan Najeriya ba
  • Lawan ya ce Najeriya fa ta talauce, babu kudi
  • Ya lashi takobin amincewa gwamnatin tarayya cin bashi a 2021

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya zama wajibi Najeriya ta cigaba da karban basussukan kudi domin aiwatar da ayyuka.

Lawan ya ce bai tunanin ya kamata gwamnati ta cigaba da tatsan yan Najeriya saboda irin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda yake hira da manema labarai bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, rahoton ChannelsTV.

Yace:

A ra'ayina, ba zai yiwu a cigaba da tastsan yan Najeriya domin smun kudin ayyuka ba; wasu kasashe na hakan, amma muna da matsala a fadin kasar nan.
Mafita daya ita ce a karbi bashi, ayi amfani da shi a hankali, kuma a tabbatar da cewa ayyukan masu dorewa ne da za'a iya biyan basussukan da su.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Shugaban Majalisa
Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa Hoto: Senate President
Asali: Facebook

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Lawan ya kara da cewa Najeriya ba ta da isasshen kudin shiga.

"Najeriya ta talauce, mu daina yaudarar kanmu. Najeriya babu kudi a halin da ake ciki," yace.

Lawan ya bada tabbacin cewa majalisar za ta amince da bukatar karban bashin da shugaba Buhari yayi idan aka dawo daga hutu a watan Yuli.

Ofishin kasafin kudi tace Ahmad Lawan yayi gaskiya

Ofishin kula da kasafin kudi na tarayya ya ce dole ne ’yan Najeriya su yarda cewa kasarsu matalauciyar kasa ce sai dai za ta iya zama attajirar kasa a gaba.

Ofishin ya kuma ce lallai ne fa kasar ta ci gaba da karbo rancen kudi domin fitar da kanta daga kangin komadar tattalin arzikin da take fama da shi.

Babban Daraktan ofishin, Ben Akabueze, ya sanar da hakan ne a zaman martani bayan kalaman da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, ya yi kan karbo bashin da kasar ke yi yayin da yake ganawa da ’yan jarida a ranar Alhamis a fadar Shugaban Kasa bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng