Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan
- Ya koka kan yadda ya ce jam’iyyar ta yi wasa da shekara hudun farko na mulkinta wajen rashin jituwa tsakanin bangarorin gwamnatin biyu
- A cewarsa, Buhari shi ne kashin bayan nasarorin da jam’iyyar ke samu
- Sai dai ya yi gargadin dole mambobin jam’iyyar su zage damtse domin nasarar gwamnatin a yanzu
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya yi gargadi da babbar murya cewar jam’iyyar APC na iya fuskantar babban kalubale idan har Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa a 2023.
Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan gargaɗin ne a cikin jawabin da ya gabatar a taron matasan Jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja ranar Talata, rahoton PT.
“Magana ta gaskiya duk wani goyon baya da muke gani Jam’iyyar APC na samu, ya samu ne ta dalilin Shugaba Muhammadu Buhari, don haka dole mu nemo mafita,’’ in ji shi.
Don haka ya ce dole ne jam’iyyar ta fara tanadi da shiri domin samun dorewar goyon bayan da ayyukan gwamnati mai ci ta hanyar tabbatar da shugabannin jam’iyyar sun mika mulki ga matasan da suka cacanta na Jam’iyyar APC.
Dole ne jam’iyya ta nemo mafita kafin karewar wa’adin mulkin Shugaba Buhari a 2023, a cewarsa.
KU KARANTA: Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu
KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997
Shugaban majalisar dattawan ya ce Buhari na da rawar da zai taka ko da ya sauka amma kuma jam’iyyar sai ta fi fuskantar babban kalubale idan ya gama mulkinsa, riwayar Arise News.
Taron matasan da APC ta gudanar shi ne irinsa na farko da ta yi tun bayan darewar jam’iyyar a mulki a 2015.
Lawan yace:
“Tsawon shekara hudu (2015 zuwa 2019), gwamnatinmu ba ta iya yin abin kirki saboda rikicin da ya faru a tsakanin Majalisar Dokoki ta Kasa - da bangaren zartarwa na gwamnati.
“Don haka, APC ta riga ta sarayar da shekara hudu masu muhimmanci. Kuma, wannan ya kamata ya kasance shekarun da ya kamata mu shawo kan 'yan Najeriya cewa sun yanke shawara mai kyau ta hanyar kawar da gwamnatin PDP a 2015.
“Mene ne mafita a wajrnmu? Mu jam’iyya daya ce a bangarorin gwamnati daban-daban. Manufofinmu ya kamata su zama iri daya. Shirye-shiryenmu da ayyukanmu ya kamata su zama iri guda, ko kuna cikin majalisa ko zartarwa.
Najeriya ta talauce
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya zama wajibi Najeriya ta cigaba da karban basussukan kudi domin aiwatar da ayyuka.
Lawan ya ce bai tunanin ya kamata gwamnati ta cigaba da tatsan yan Najeriya saboda irin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda yake hira da manema labarai bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, rahoton ChannelsTV.
Asali: Legit.ng