Abin da rundunar 'yan sanda ta ce kan zargin da Gumi ya yi na cewa jami'an tsaro na taimakon 'yan bindiga

Abin da rundunar 'yan sanda ta ce kan zargin da Gumi ya yi na cewa jami'an tsaro na taimakon 'yan bindiga

  • Rundunar yan sandan Nigeria ta ce ba za ta yi tsokaci kan zargin da Sheikh Gumi ya yi ba na cewa jami'an tsaro na taimakawa yan bindiga
  • Mai magana da yawun yan sandan Nigeria, Frank Mba ya ce bai yi nazarin kalaman Gumi ba don haka bai san ainihin abinda ya ke nufi ba
  • Frank Mba ya kara da cewa abin da ya ji Gumi ya ce shine 'jami'an tsaro' don haka bai ma tabbatar ko yan sanda ya ke nufi ba

Rundunar yan sandan Nigeria ta ce ba za ta yi tsokaci ba a kan zargin da Sheikh Ahmad Gumi ya yi na cewa jami'an tsaro suna aiki tare da 'yan bindiga, rahoton Daily Trust.

Fitaccen malamin addinin musuluncin ya yi wannan zargin ne a lokacin da aka yi hira da shi a Arise TV a ranar Laraba da safe.

Kakaki yan sanda Frank Mba
Mai magana da yawun yan sandan Nigeria, Frank Mba
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

A yayin da ya ke cewa yan bindigan kasuwanci suke yi, malamin ya ce, "Yan bindigan nan, idan baka sani ba suna aiki tare da baragurbi cikin jami'an tsaron mu. Wannan kasuwanci ne. Don haka akwai hannun mutane da dama a ciki, za ka yi mamaki."
"An kama su a Zamfara; an kama su a ko ina, ta yaya suke shigo da manyan makamai da iyakokin mu? Ta yaya wannan manyan makaman ke shigowa kasar mu suna shiga dazuka idan ba tare da hadin kan wasu bata gari cikin jami'an tsaro ba? Ba zai yi wu ba."

Amma da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan Frank Mba, ya ce ba zai yi tsokaci a kan abin da Gumi ya fada ba sai ya yi nazari kan abin da ya ke nufi.

DUBA WANNAN: Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan sun kwankwaɗar wani maganin gargajiya

"Bani da abin cewa. Ayyuka sun min yawa. Ba zan iya magana a kan lamarin ba. Ban yi nazarin ainihin abin da mutumin ya ce ba, na abin da ya ke nufi da kalaman. Da naga 'jami'an tsaro', ban san ko yana nufin yan sanda bane. Ba zan iya cewa komai ba a yanzu."

Abinda rundunar sojoji ta ce:

Kazalika, da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu, ya ce rundunar sojojin za ta yi martani a kan lamarin.

Yan bindiga da barayin shanu sun dade suna adabar mutane musamman arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel