Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan kwankwaɗar wani maganin gargajiya

Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan kwankwaɗar wani maganin gargajiya

  • Wasu mutane 10,fulani, yan gida daya sun mutu bayan shan maganin gargajiya a jihar Kwara
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane biyu ne suka bada maganin suka ce kowa a gidan ya sha
  • Rundunar yan sanda ta kama mutane biyun da suka bada maganin gargajiyar ta kuma fara zurfafa bincike

Mutane 10 yan gida daya a garin Gwanara a karamar hukumar Baruteen na jihar Kwara sun riga mu gidan gaskiya bayan sun sha wani maganin gargajiya a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Abin bakin cikin ya jefa mutanen garin na Baruteen da mafi yawancinsu Fulani ne cikin dimuwa da damuwa.

Maganin gargajiya
Maganin gargajiya. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane 3 da ke shiga irin ta NDLEA sun faɗa komar 'yan sanda a Jigawa

Ba a samu cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru ba a lokacin hada wannan rahoton.

Wasu yan garin da aka yi magana da su a wayan tarho sun ce garin na da nisa sosai daga babban birnin jihar, Leadership ta ruwaito.

A cewarsu, fulanin da abin ya faru da su ba masu yawo bane, asalinsu yan garin Kaiama ne.

Karamar hukuma ta tabbatar da afkuwar lamarin

Da aka tuntube shi, shugaban kwamitin riko na Baruteen, Abdulrashid Ibrahim ya shaidawa Daily Trust cewa ya aika da tawaga a ranar Talata don su yi bincike amma har yanzu ba su dawo ba.

Ya ce:

"Ka san wurin da nisa. Tuni na aika tawaga na jami'an tsaro da masu bada taimako.
"Har yanzu safen ranar Laraba, muna jiran dawowarsu.
"Abin da muka sani shine su Fulani ne da suka sha jiko da ake zargin ya kashe dukkansu 10. Idan tawagata ta dawo, za mu yi karin bayani kan lamarin."

Yadda abin ya faru

Rundunar yan sandna jihar Kwara ta bakin kakakinta, Ajayi Okasanmi ta ce wani Ibrahim Bonnie daga rugar Fulani na Biogberu, Gwanara cewa wani Okosi Musa da Worugura Junlin sun zo wurin mahaifiyarsa, Pennia Bonni a rugarsu suka bata maganin ciwon kafa.

Ajayi ya ce:

"Sun kuma umurci ta tabbatar kowa a gidan ya sha maganin domin kada su harbu da ciwon kafar, bayan shan maganin sai suka fara mutuwa daya bayan daya har da mahaifiyar mai ciwon kafan."

Kwamishinan ya sanda, Mohammeed Lawal Bagega ya bada umurnin a yi bincike sannan wadanda ake zargin suna taimakawa rundunar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164