An yi amfani da bokitai don tare ruwan sama da ke zuba daga rufin Majalisar Nigeria

An yi amfani da bokitai don tare ruwan sama da ke zuba daga rufin Majalisar Nigeria

  • Rahotanni da ke fitowa na nuna cewa wasu sashi na rufin Majalisar Tarayya na bukatar gyara bayan ruwan sama ya lalata shi
  • An dakatar da zaman majalisar na wani lokaci amma an cigaba bayan ma'aikatan majalisar sun gyara wurin da ruwan ke zuba
  • Ba a taba yi wa majalisar tarayyar babban gyara ba tun lokacin da aka gina shi kimanin shekaru 27 da suka gabata

Ruwan sama ya lalata wani sashi na harabar majalisar tarayyar Nigeria a safiyar ranar Talata 22 ga watan Yunin shekarar 2021.

The Punch ta ruwaito cewa barnar da ruwan saman ya yi ya janyo ruwa na ta zubowa daga rufin majalisar yana shiga wani sashi cikin inda yan majalisar ke zama.

Ma'aikatan Majalisar Tarayyar Nigeria, NASS, suna goge ruwan zama da ke yoyo daga rufin majalisa
Ma'aikatan Majalisar Tarayyar Nigeria, NASS, suna goge ruwan zama da ke yoyo daga rufin majalisa. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

Afkuwar lamarin ya janyo an yi jinkirin fara zaman yan majalisar da suka dawo daga hutun mako daya a yau Talata.

The Nation ta ruwaito cewa masu shara da goge-goge sun saka robobi da bokiti sun tare wuraren da ruwan ke zubowa.

Vanguard ta wallafa bidiyon yadda abin ya faru a shafinta na Facebook da ke nuna ma'aikatan suna kwalfe ruwan suna saka wa cikin bokiti sannan suna goge-goge.

KU KARANTA: Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Majalisar tarayyar ta amince da ware kudi Naira biliyan 37 domin yin gyara da kwaskwarima a majalisar da aka gina kimanin shekaru 27 da suka gabata.

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar a siyo mata tsintsiya guda miliyan uku daga masu siyarwa a kasuwanni don sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Calabar.

Mr Ita ya ce an gano kwastam an samu karancin tsintsiya a jihar, wanda shine alama na jam'iyyar, bayan mutane da yawa sunyi tururuwan shiga jam'iyyar bayan gwamnan jihar Ben Ayade ya shigo jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel