Bikin karɓar gwamnan PDP: APC ta bada kwangilar siyan tsintsiya miliyan uku

Bikin karɓar gwamnan PDP: APC ta bada kwangilar siyan tsintsiya miliyan uku

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar siyo mata tsintsiya miliyan uku
  • Sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bada sanarwar a ranar Laraba a Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers
  • Jam'iyyar ta ce ta bada kwangilar siyo tsintsiyar ne saboda karancin tsintsiya da ake fuskanta a jihar bayan gwamna Ben Ayade da wasu manyan yan siyasa sun koma APC

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar a siyo mata tsintsiya guda miliyan uku daga masu siyarwa a kasuwanni don sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Calabar.

Magoya bayan APC dauke da tsintsiya
Magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress, APC dauke da tsintsiya. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

Dalilin bada kwangilar siyo tsintsiyar

Mr Ita ya ce an gano kwastam an samu karancin tsintsiya a jihar, wanda shine alama na jam'iyyar, bayan mutane da yawa sunyi tururuwan shiga jam'iyyar bayan gwamnan jihar Ben Ayade ya shigo jam'iyyar.

Domin magance wannan kalubalen, jam'iyyar ta bada kwangilar siyo tsintsiya miliyan uku daga masu sayarwa a garin domin biyan bukatun masu bukatar tsintsiyar.

"Kowa ya san cewa canji ya zo jihar mu bayan gwamnan mu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar mu.
"Yanzu abin da ke faruwa shine an samu karancin tsintsiya a Cross Rivers a yayin da miliyoyin mutane ke cigaba da tururuwa suna shigowa jam'iyyar mu.

KU KARANTA: Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

"A karshen makon da ya gabata, ciyamomi, kansiloli, yan majalisar jihar da na tarayya tare da magoya bayansu 100,000 a kananan hukumomin Bekwarra, Ikom da Etung sun shigo jam'iyyar mu," ya kara da cewa.

A wani labarin, wasu masu zanga-zanga a Umaru Yar'Adua Way, babban birnin tarayya Abuja, a safiyar ranar Litinin sun banka wuta a kan titi, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito.

Titin na Musa Yar'Adua Way ne ake bi idan za a tafi filin tashi da saukan jiragen sama a birnin tarayyar Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar suna ta ihu cewa 'Buhari Must Go' ma'ana 'Dole Buhari Ya Tafi' yayin da suke dauke da takardu masu rubutu daban-daban na nuna rashin kaunar kasancewar shugaban kasar a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel