Da Dumi-Dumi: Wani Jigon Jam'iyyar APC Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Da Dumi-Dumi: Wani Jigon Jam'iyyar APC Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Wani babban jigon jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Eti-Osa ta gabas, jihar Lagos, ya rigamu gidan gaskiya
  • Hon. Olatunji, ya kasance shugaban ƙaramar hukumar Eti-Osa kafin rasuwarsa ranar Litinin da daddare
  • Ya kuma lashe zaɓen tsayar da ɗan takara a ƙarƙashin APC, inda ya zama ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen dake tafe a jihar

Shugaban ƙaramar hukumar Eti-Osa ta gabas, jihar Lagos, Olufunmi Rafiu Olatunji, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta gano cewa Olatunji yayi fama da rashin lafiya kafin rasuwar tasa ranar Litinin da daddare.

KARANTA ANAN: Bana Son Sake Jin Yan Bindigan da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Gargadi Yan Sanda

Yayin tabbatar da mutuwar Olatunji ranar Talata da safe, kakakin marigayin ya bayyana cewa:

"Da ƙuna a cikin zuciyar mu amma mun miƙa lamarin mu ga Allah, Muna sanar da rasuwar baban mu, ɗan uwan mu, abokin mu, mai ƙoƙarin kawo cigaban ƙasa, Hon. Olufunmi Rafiu Olatunji, bayan fama da rashin lafiya."

Olufunmi Rafiu Olatunji
Da Dumi-Dumi: Wani Jigon Jam'iyyar APC Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

"Marigayin ya kasance zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Eti-Osa kafin mutuwarsa da daren ranar Litinin 21 ga watan Yuni, 2021."

"Za'a gudanar da jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanazar, muna masa fatan samun rahama maɗaukakiya wato aljannatul firdausi."

KARANTA ANAN: Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Kafin rasuwarsa ya lashe zaɓen tsayar da ɗan takara a APC

Kafin rasuwar Hon. Olatunji, yana neman sake komawa kujerarsa ta shugaban ƙaramar hukuma ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Kuma ya lashe zaɓen tsayar da ɗan takara ƙarƙashin APC da ƙuri'u 1977, inda ya zama ɗan takarar APC a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Lagos dake tafe ranar 24 ga watan Yuli.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da gina jami'o'i guda biyar a faɗin Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Sakataren ma'aikatar ilimi ta ƙasa, Arch Sonny Echono, shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel