Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da gina jami'o'i guda biyar a faɗin Najeriya
  • Sakataren ma'aikatar ilimi ta ƙasa, Arch Sonny Echono, shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja
  • Yace shugaban ya amince da fidda kuɗaɗe daga asusun TETFund domin fara aikin cikin gaggawa

Shugban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kafa sabbin jami'o'i guda biyar a Najeriya, waɗanda zasu maida hankali a ɓangaren lafiya da fasahar zamani, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya

Shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin cike babban gurbin likitoci masu duba marasa lafiya, binciken lafiya da kuma samar da magunguna.

Hakazalika Buhari ya amince da fitar da biliyan N4bn na farawa ga jami'o'in fasaha da kuma biliyan N5bn ga jami'o'in kimiyyar lafiya daga asusun TETFund domin tabbatar da anfara aikin da wuri.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

Sakataren dindin na ma'aikatar ilimi, Arch Sonny Echono, shine ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

Yace shugaba Buhari ya amince da kafa sabbin jami'o'in fasaha guda biyu a jihohin Jigawa da Akwa Ibom.

Ya ƙara da cewa shugaban ya amince da gina makarantar fasaha ta tarayya (NIT) da kuma jami'o'in lafiya da kimiyyar likitanci guda biyu a Azare, jihar Bauchi da Ila Orangun, jihar Osun.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Buhari ya amince da inganta wasu jami'o'in fasaha

Echono ya bayyana cewa shugaba Buhari ya amince da gyara da inganta jami'o'in fasaha guda hudu dake Akure, Yola, Owerri, da Minna.

Echono, yace: "Za'a gina sabbin jami'o'in fasaha a shekarar 2021 yayin da sauran waɗanda za'a gyara tare da sabuwar babbar makarantar fasaha (NIT) za'a yi aikin su a shekarar 2022."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya roƙi kamfanin sadarwa na MTN ya sauƙaƙa wa yan Najeriya masu amfani da layukan su, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Buhari yace Najeriya ce ƙasa ta uku a duniya da kamfanin ya fi samun kuɗaɗen shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262