PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna
- INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbin da ta gudanar a mazaɓar Sabon Gari, Zaria, jihar Kaduna
- Baturen zaɓen yankin, Dr. Muhammed Musa, ya bayyyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe
- An gudanar da zaɓen cike gurbin ne biyo bayan ƙauracewa ayyukan majalisa da ɗan majalisar yankin yayi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta bayyana Alhaji Usman Baba na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakilta mazaɓar Sabon Gari.
Baturen zaɓen yankin, Dr Mohammed-Nuruddin Musa, shine ya faɗi sakamakon zaɓen ranar Asabar a Zaria, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Mu Haɗu a Filin Yaƙi, Gwamna Yayi Alƙawarin Shiga Daji Domin Yaƙi da Yan Bindiga
Yace Baba na jam'iiyar PDP ya lashe zaɓen da ƙuri'u 9,113, yayin da ya kayad da babban abokin gwabzawarsa, Malam Musa Musa, na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 7, 404, kamar yadda channels tv ta ruwaito
Baturen zaɓen yace: "Alhaji Usman Baba na jam'iyyar PDP, shine ya lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majaƙisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari."
Dr. Musa ya ƙara da cewa, Malam Anas Abdullahi, na jam'iyyar ADC ya samu ƙuri'u 62; Chindo Ibrahim, na jam'iyyar ADP ya samu kuri'u 61, yayin da Musa Halilu na PRP ya samu ƙuri'u 304.
KSRANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC a Kebbi Sama da 80
Majalisar dokokin Kaduna ta bayyana kujerar a matsayin babu kowa
Hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an gudanar da zaɓen cike gurbin ne biyo bayan bayyana kujerar a matsayin babu mai riƙe da ita da majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi.
Hakan ta faru ne saboda ƙauracewa ayyukan majalisar dokoki da ɗan majalisa mai wakiltar Sabon gari, Aminu Shagali, yayi na tsawon kwanaki 365.
A wani labarin kuma Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane
Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun yayi alƙawarin rushe duk wani gida da aka kama masu garkuwa na boyewa a cikinsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana zaman lafiya a jiharsa kuma su samu mafaka a cikinta ba.
Asali: Legit.ng