Mu Haɗu a Filin Yaƙi, Gwamna Yayi Alƙawarin Shiga Daji Domin Yaƙi da Yan Bindiga
- Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, yayi alƙawarin shiga cikin daji domin yaƙi da yan bindiga a jiharsa
- Bagudu yace addini ya amince a sadaukar da rayuwa domin kare martaba, dukiya da imani
- Shugaban ƙungiyar gwamnoni NGF, Fayemi, ya jajantawa al'ummar jihar Kebbi kan lamarin satar ɗaliban FGC
Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, yayi alƙawarin shiga cikin mafarauta domin bin sawun yan bindigan jihar, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Da yake jawabi ga mafarauta dake taimakawa wajen yaƙi da rashin tsaro, Gwamna Bagudu wanda yake tare da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, yace da zaran ya samu rahoton tsaro daga jami'an soji, zai haɗe da maharauta a filin yaƙi.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Wasu Fusatattun Matasa Sun Rufe Hanyar Kaduna-Abuja
Gwamnan yace: "Zamu fita yaƙi, kuma kamar yadda na yi alƙawari, duk ranar da zan fita ba za'a ganni a ofis ba. Kuma akwai wasu gwanonin da zasu baro mutanen su, su zo mu shiga filin yaƙi da su."
"Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, tare da jami'an tsaro suna iya bakin kokarin su. Amma duk da haka muna buƙatar mu shirya kan mu, mu sanya kaki, mu tinkari waɗannan yan ta'addan."
"Addinin musulunci da na kiristanci ya bamu damar sadaukar da rayuwar mu wajen kare martabarmu, dukiyoyin mu da imanin mu."
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80
Fayemi ya jajantawa Gwamnati da mutanen Kebbi kan satar ɗaliban FGC
Da yake jawabi ga mafarautan, Fayemi yace yazo jihar ne a bisa wakilcin ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa NGF.
Yace: "Mun zo nan ne domin jajantawa ɗan uwanmu, Gwamna Atiku Bagudu da kuma al'ummar jihar Kebbi kan abu mara daɗi da ya faru a makarantar FGC Birnin Yauri."
A wano labarin kuma Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani
Hukumar yan sanda tace har yanzun ba ta gano adadin ɗaliban da yan bindiga suka sace a jihar Kebbi ba, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Kakakin yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, shine ya bayyana haka ranar Jumu'a a Birnin Kebbi.
Asali: Legit.ng