EFCC ta kwato N6bn, Gidaje 30, Motoci 32 a cikin watanni 3 - Bawa

EFCC ta kwato N6bn, Gidaje 30, Motoci 32 a cikin watanni 3 - Bawa

  • Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kwato makudan kudade tare da wasu kayyakin
  • Kadarorin da aka kwato ba duka bane ya ke mallakin Gwamnatin Tarayya
  • Daga farkon mulki zuwa yanzu an samu kiyasin kudi da aka kwato kimanin miliyan shida tare da kudin wasu kasashe

Hukumar yaki da cin hancin tattalin Kasa ta ce kawo yanzu ta gano sama da Naira biliyan 6, da gidaje 30 da motoci 32 tsakanin watan Maris zuwa Yunin bana.

Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin taron karawa juna sani na mako-mako da Kungiyar Tattaunawar Shugaban Kasa ta shirya.

Bawa ya ce:

“Daga lokacin da na karbi mulki, mun kwato sama da Naira biliyan 6, sama da dala miliyan 161, sama da fam 13,000, € 1,730, dalar Kanada 200, CFA 373,000, ¥ 8,430.
"Mun kwato Gidaje kimanin guda 30, kafet daya, kayan lantarki 13, Gona daya, masana'anta daya, babura biyu, gidan mai daya da kuma motoci kimanin 32."

DUBA NAN: ‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

Shugaban Bawa
EFCC ta kwato N6bn, Gidaje 30, Motoci 32 a cikin watanni 3 - Bawa Hoto: EFCC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

A cewarsa, ba duka kudaden da hukumar ta gano ba ne ke shiga asusun Gwamnatin Tarayya.

Yace:

“Zan yi amfani da wannan damar don bayyana wasu batutuwa. Akwai kadarori da dama da Hukumar EFCC ta bankado a tsawon shekaru amma ba duka ba ne mallakin Gwamnatin Tarayya.

“Mun sake gano wadanda yan fashi su kayi ma kwamushe kuma zai iya zama mutane ma banbanta, kananan hukumomi, gwamnatin jihar, gwamnatin tarayya, ko kamfanoni a Najeriya ko a Kasashen ketare.

An kwato kudi daga wajen tsohon kamfanin Atiku

A bangare guda, Shugaban EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce sun yi nasarar karbo wasu kudi har $100m a madadin NPA.

Abdulrasheed Bawa ya na cewa sun karbo wadannan makudan kudi a hannun kamfanin Integrated Logistics Services (INTELS).

Bawa ya ce ba gwamnatin tarayya kadai hukumar EFCC ta ke yi wa aiki, ya ce suna karbo hakkin duk wani da aka yi wa satar kudi ko wata dukiya a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel