Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

  • Malam Bawa ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da karanta labarai ta intanet su koma karanta jaridu saboda rashin ingancin labaran intanet
  • Dattijon da ke zama a Zariya da ya shafe shekara 51 yana sana’ar ya koka yadda cinikin jaridun ya yi kasa tun bayyanar intanet da soshiyal midiya
  • Ya fada a cikin hirar cewa ya yi aure ya gina gida sannan ya dauki nauyin ‘ya’yansa 15 a sana’ar sayar da jaridun

Wani dan Najeriya ya koka game da yadda kasuwar jaridu ke zagwanyewa a cikin shekarun nan sakamakon bayyanar kafofin yada labarai na intanet.

Mutumin mai suna Malam Bawa wanda yake sana’ar sayar da jaridu ya fada wa Sashen Pidgin na BBC cewa ya fara sana’ar tun shekara 51 da suka gabata.

“Intanet ya kwace mini hanyar samun abinci,” kamar yadda ya koka.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da karanta labarai ta shafukan intanet saboda a cewarsa labaran da ake wallafa wa a intanet ba su da inganci. Don haka ya bukaci kowa ya koma karanta labaran da ake wallafa wa a jaridun.

Dattijon wanda ya fara sana’ar sayar da jaridun tun bayan kawo karshen yakin basasar Najeriya ya ce ya samu nasarori da dama ta dalilin sana’ar.

Ya ce ya mallaki gida na kansa ya kuma yi aure sannan ya dauki dawainiyar ‘ya’yansa 15 daga abin da yake samu a kasuwancin jarida.

DUBA NAN: ‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida
Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida Hoto: BBC Pigdin
Asali: Instagram

KU KARANTA: Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

Sai dai ya kuma koka kan yadda duk da shekarun da ya shafe yana gudanar da sana’ar har yanzu babu wani kamfanin jaridar da ya ga dacewar ya yi wani abin karrama shi.

Masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani sun mayar da martani kan kiran da ya yi cewa a koma karanta labaran da ake wallafa wa a jaridun.

Mutane a Soshiyar Midiya sun yi tsokaci

Wani mai amfani da sunan @xwaggaruns ya ce:

"Ka rungumi sauyi… Nan gaba kadan motoci masu amfani da lantarki za su fara bayyana a cikin Najeriya… Man fetur kansa zai zama tsohon yayi kuma shi ne silar karshen siyasar Najeriya a duniya.”

Wani ma da ke amfani da sunan @sparklesjewelries ya wallafa:

"Aaaayaaa.... Inda ya ce babu kamfanin jaridar da ya da ya yi masa wani abu domin nuna godiya ga dadewarsa yana sana’ar, abin ya sosa mini rai.”

Wani mai amfani da sunana @toesscene ya rubuta:

"Eeya.... Alal akalla dai ya samu damar yin wani abin arziki san da ya samu kudin. Yanzu ‘yan’yan ne ya kamata su kula da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel