Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

  • Kudin wutar lantarki a Najeriya yayi kadan sosai a kasar, kuma hakan yana shafar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Babban Bankin Duniya ya ce Gwamnatin Najeriya na kashe makudan kudade wajen samar da wutan lantarki
  • Bretton Woods ya ce masu hannu da shuni a Najeriya sun fi cin gajiyar karancin haraji a kasar, inda masu karamin karfi ke karban abunda be kai haka ba

Hukumar Global Monetary Authority ta ce harajin da aka daura ma 'yan Najeriya ba ya nuni da irin kudin da kamfanin samar da lantarki da kuma kamfanin da take rarraba wutan.

An bayyana hakan ne a cikin rahoton 'Bangaren sake fasali' wanda Bankin Duniya ya fitar a ranar Talata, cewa an kashe sama da tiriliyan N1.68 a kan karin mafi karanci kudin harajin wuta daga shekaran 2015 zuwa 2019 wanda Shugaban kasa yayi

Babban Bankin Duniya ya ce kashi 40% na masu hannu da shuni a Najeriya su ke cin kashi 80% na kudin haraji da ake kashewa.

Masu hannu da shuni a Najeriya su suka fi cin gajiyar ƙarancin kuɗin haraji wannan na nufin' cewa yan Nijeriya suna biyan kuɗin wutar lantarki ƙasa da abunda ake samarwa.

DUBA NAN: ‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum Read more: https://hausa.legit.ng/1421002-ka-matukar-burge-ni-inji-buhari-bayan-da-ya-bude-ayyuka-7-cikin-556-na-gwamna-zulum.html

Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya
Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

Ya kara da cewa:

"Kashi takwas ne kawai ke amfana da kaso 40 cikin 100, sannan kasa da kashi biyu ke amfanar da talakawa ."
"Kudaden da aka kashe domin samar da tallafin domin ya amfanar da masu karamin karfi don more wuta na da matuka yawa, amma sai ya kasance tallafin Gwamnati mafi tsoka yafi karkata ga wadanda ba sa bukatar taimako wajen biyan kudi."

Shugaba Buhari ya ari kudi kimanin Naira tiriliyan 1.3 don tabbatar da ci gaban samar da wutar lantarki da rarrabawa a fadin kasar.

Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

Kasa da kwanaki uku bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa mulkinsa ya tsamo mutum miliyan 10 daga talauci, bankin duniya ya ce tashin farashin kayan abinci ya tsoma mutane miliyan bakwai cikin fatara, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ikirarin na shugaban kasan da na bankin duniyan ya zo ne a yayin da hukumar kididdiga ta kasa ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya sauka da kashi 0.19 a watan Mayun 2021 yayin da kuma 'yan Najeriya ke ta kokawa kan hauhawar ababen bukata na rayuwa kamar abinci, magunguna da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel