Budurwa ta hada baki da saurayinta domin karyar an yi garkuwa da ita, ta nemi fansar N500,000

Budurwa ta hada baki da saurayinta domin karyar an yi garkuwa da ita, ta nemi fansar N500,000

  • Yar shekara 16 ta yi karyan an yi garkuwa da ita
  • Bayan tayar da hankalin iyayenta, ta bukaci dubu dari biyar kudin fansa
  • Ita da saurayin na ta da suka shirya abin sun shiga hannun hukuma

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Ekiti ta kama wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Abimbola Suluka tare da saurayinta mai suna Oluwaseun Olajide kan zargin hada baki da yin garkuwa da kansu.

Ana zargin Abimbola da game baki da saurayinta dan shekara 25 tare da wadansu abokansa guda biyu wajen shirya garkuwar domin samun kudi.

Kakakin ‘yan sandan Sunday Abutu cikin wata sanarwa a ranar Juma’ah ya bayyana cewa ‘yar uwar Abimbola ta kai wa caji ofis rahoton cewa ‘yar uwarta ta bace bat a kan hanyarta ta zuwa makaranta daga gida, riwayar ChannelsTV.

A cewar Abutu ‘yar uwar ta ce da aka kira lambar wayar Abimbola sai wani wanda ba a san ko wane ne ba ya amsa kiran inda ya shaida musu cewa Abimbola tana a hannunsu yanzu kuma ba za su sako ta ba har sai an bada fansar Naira dubu 500.

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Budurwa ta hada baki da saurayinta
Budurwa ta hada baki da saurayinta domin karyar an yi garkuwa da ita, ta nemi fansar N500,000 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Dubunsu ta cika ne a lokacin da rundunar musamman domin yaki da garkuwa da mutane ta binciko bayanan asusun wanda za a tura wa kudaden fansar inda ta gano mabuyarsu a wani otel sannan ta kamo saurayin da yarinyar a wani otel cikin babban birnin jihar inda aka ajiye Abimbola a matsayin wacce aka yi garkuwa da ita.

Abimbola da ma sauran samari ukun duk sun amince da aikata da laifin, tana mai kafa hujjar aikata hakan da cewa tana son tara kudaden ne daga danginta domin ta kaura daga jihar sakamakon yadda mahaifiyarta ta tilasta mata sai ta karanta aikin likita yayin da ita kuwa take son zama jarumar fina-finai.

An ceto wasu cikin daliban FGC Yauri

Malamai da daliban kwalejin gwamnatin tarayya dake Yawuri a jihar Kebbi, wadanda jami'an tsaro suka ceto daga hannun 'yan bindiga a sa'o'in farko na ranar Juma'a, a halin yanzu suna asibiti inda ake kula da lafiiyarsu.

'Yan bindiga sun kutsa makarantar a ranar Alhamis kuma sun sace dalibai da malamai.

Bayan aikin jami'an hadin guiwa na tsaro, malamai biyu da dalibai biyar sun kubuta yayin da wata daliba mace ta mutu a harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel