Hotunan daliban Kebbi da jami'an tsaro suka ceto daga wurin 'yan bindiga kwance a asibiti
- Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ziyarci dalibai da malaman kwalejin tarayya ta Yawuri da aka ceto daga hannun 'yan bindiga
- Daliban biyar da malaman biyu suna kwance a babban asibitin Yawuri inda suke karbar taimakon likitoci
- A yayin cetosu daga hannun 'yan bindiga, an rasa rayuwar daliba daya yayin da sauran suka jigata da raunika
Malamai da daliban kwalejin gwamnatin tarayya dake Yawuri a jihar Kebbi, wadanda jami'an tsaro suka ceto daga hannun 'yan bindiga a sa'o'in farko na ranar Juma'a, a halin yanzu suna asibiti inda ake kula da lafiiyarsu.
'Yan bindiga sun kutsa makarantar a ranar Alhamis kuma sun sace dalibai da malamai, The Cable ta ruwaito.
Bayan aikin jami'an hadin guiwa na tsaro, malamai biyu da dalibai biyar sun kubuta yayin da wata daliba mace ta mutu a harin.
KU KARANTA: Bidiyon bikin soja mace, ana kada ganga tare da mika mata takobi
Har yanzu gwamnatin jihar bata tabbatar da yawan wadanda aka sace ba ko kuma wadanda ke hannun 'yan bindigan a halin yanzu.
A ranar Juma'a, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya kai ziyara babban asibitin Yawuri inda aka kwantar da dalibai da malaman da aka ceto, The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA: Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar
Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga kafin harin makarantar Yauri – Gwamna Bagudu
Atiku Bagudu, gwamnan Kebbi, ya ce daga rahotannin da ya samu, ‘yan fashin da suka kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri, sun shigo a daruruwan su.
'Yan bindiga, a ranar Alhamis, sun mamaye makarantar sannan suka yi awon gaba da adadin dalibai da malamai da ba a tabbatar ba.
A wani labari na daban, wata cikakkiyar likita ta sheka lahira bayan wasu 'yan bindiga sun harbeta a kauyen Salka dake karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro cewa wasu miyagun 'yan bindiga ne da zasu kai su biyar suka kaiwa likitan farmaki har asibitin da take aiki.
Makwabtan garin sun ce daya daga cikin makasan ya shiga asibitin kuma ya bukaci ganin likitan sannan suka tasa ta gaba zuwa wani wuri na daban.
Asali: Legit.ng