Zan Cikawa yan Najeriya Dukkan alkawurran da na dauka lokacin Zabe - Buhari

Zan Cikawa yan Najeriya Dukkan alkawurran da na dauka lokacin Zabe - Buhari

  • Shugaba Buhari ya dauki alkawura da dama a lokacin gangamin neman zabe a shekara ta 2015
  • Tabarbarewan tsaro da kuma tattalin arziki suna cikin muhimman abubuwan da aka alkauranta
  • Kungiyar Muhammadu Buhari da Osinbanjo Dyynamic ta ziyarci fadar Shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai cika dukkan alkawuran da ya dauka a Shekarar 2015.

Duk da yawan tabarbarewar tsaro da ake fama da shi a kusan dukkan sassan kasar nan da kuma kalubalen tattalin arziki da 'yan Najeriya da dama ke fuskanta, Shugaba Buhari ya kuma ce zai cika dukkan manufofin Gwamnatinsa.

Jaridar Ptimes ta ruwaito yadda shugaban ya gaza wajen tabbatar da tsaro a kasar nan da kuma tabbatar da tsare lafiyar ‘yan kasar shekaru bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Hakazalika Buhari gaza wurin tabbatar da daidaituwar tattalin arziki shekaru shida bayan da aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa. Tabarbarewan tattalin arziki, tsaro, yaki da cin hanci rashawa sune manyan alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya lokacin da yake gangamin neman kuri'a.

Yanzu haka yana wa'adin mulkinsa na biyu wanda zai kare a 2023.

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Zan Cika Dukkan alkawurran Da na dauka lokacin Zabe - Buhari
Zan Cika Dukkan alkawurran Da na dauka lokacin Zabe - Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa da ke Abuja lokacin da ya karbi bakwancin mambobin kungiyar Muhammadu Buhari da Osinbajo Dynamic Support Group.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kungiyar ta je Villa ne don gabatar da littafin su ga Shugaban Kasa mai taken - (Takardar nasarori 5 da gwamnan Muhammadu Buhari ta samu tsakanin 2015-2019).

Buhari yace:

“Jami’an MBO da kuma mambobin kungiyar sun ga kyawawan ayyukan da muke gudanarwa daga lokacin da muka karbi ragama a shekarar 2015.
"Wadannan ayyukan ne suka sa aka samar da littafin, kuma ina fatan cewa 'yan Nijeriya za su yaba kwazon da wannan Gwamnatin ta yi yayin da ake ci gaba da yin aiki ba kakautawa."

Mutanen jihar Borno sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari tarba da arziki

Shugaba Muhammmadu Buhari, a ranar Alhamis 17 ga watan Yuni ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar da na tarayya suka yi.

Shugaban kasar kuma ya yi amfani da wannan damar domin ganawa da dakarun sojojin Nigeria da ke fafatawa da yan Boko Haram a jihar ta arewa maso gabashin Nigeria.

Ba kamar ziyarar da ya kai a Fabarairun 2020 inda wasu mazauna jihar suka yi masa ihu ba, wannan karon an masa tarbar ban girma inda mutane suka yi layi a gefen titi suna ta masa jinjina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel