Na kan samu N400,000 a wata - Mai kaiwa yan bindiga Burodi a jihar Kaduna

Na kan samu N400,000 a wata - Mai kaiwa yan bindiga Burodi a jihar Kaduna

  • Hukuma tayi sa'ar chafke masu kaima ma yan ta'adda burodi a sansaninu
  • Hassan Magaji mamalakin Gidan Burodi, Ya fi samun riban siyarwa yan fashi akan saidawa sauran mutane
  • Akwai hatsari a tattare da kaima yan fashi burodi dan ana iya kame a kowani lokaci

Hukumar yan sanda ta cika hannu da masu kaiwa yan bindiga Burodi ranar 8 ga Yuni yayinda suka nufi shiga dajin Damari, yankin karamar hukumar Birnin Gwari.

Wadanda ake zargin su ne Hassan Magaji, Abubakar Ibrahim, Auwal Abubakar da Ibrahim Kabiru an kamasu ne a ranar 8 ga Yuni da misalin karfe 5 na yamma yayin da suke kan hanyar su na zuwa Dajin Damari don kai biredin da ake zargin na ’yan fashi ne.

Jaridar Saturday Sun ta labarin cewa jami'in ya sun yi aiki ne bisa bayanan sirri da suka samu cewa, wadanda ake zargin suna kai kayan abinci tare da kai rahoton bayanai ga 'yan ta'addan a sansanonin Galadimawa, Damari, Kidandan da na Awala duk a kan iyakar Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa a Kaduna.

Wadanda ake zargi sun kai ‘yan sanda masana’antar inda aka gano burodi kimanin guda 150.

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Na kan samu N400,000 a wata - Mai kaiwa yan bindiga Burodi a jihar Kaduna
Na kan samu N400,000 a wata - Mai kaiwa yan bindiga Burodi a jihar Kaduna
Asali: Facebook

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Mamallakin Gidan Biredin, Hassan Magaji a wata hira da aka yi da shi ya shaidawa Jaridar Saturday Sun cewa ya fara kai wa 'yan fashin burodi ne lokacin da ya fahimci cewa ita ce hanya mafi sauki da zai sayar da kayayyakinsa a kan farashi mafi tsada.

Abun da ya ke fadi:

“Ni shekaru na 29 kuma haifaffen ƙauyen Galadimawa da ke Jihar Kaduna. Na yi aure da mata biyu Allah ya albarkace ni da yara uku. Da babur nake ja ina kasuwanci amma sai na fahimci abun babu riba saboda masu sata. Sun sha kwacemin babur.
“Kwatsam wani dan uwana, Mustafa Magaji wanda ke da gidajen burodi da dama, ya kawo min ziyara a shekarar 2018 inda ya koya min yadda ake gasa biredin. Nayi amfani da N21, 000 wanda na yi kokari na tara domin fara kasuwancin kuma a yanzu ina samun akalla N400, 000 a wata. Bunkasar kasuwanci na ya fara ne lokacin da na fara samar da burodi ga 'yan ta'adda.

Gwamnan APC ya ambaci abinda ke haddasa rashin tsaro a Najeriya

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya gano rashin amana da adalci a matsayin wani bangare na dalilan da ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, a yayin bude taron tattaunawar masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu game da batun samar da zaman lafiya ga jihohin Taraba, Benuwai da Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel