Muna Zawarcin Yan Bindiga a Kebbi Ruwa a jallo - Yan Sanda

Muna Zawarcin Yan Bindiga a Kebbi Ruwa a jallo - Yan Sanda

  • Kimanin Malamai uku ne aka sace tare da daliban da ba'a san iya adadisu ba tare da hallaka jami'in tsaro daya
  • Kwamishinan yan sanda jihar Kebbi CP Adeleken ya ce Mutanen gari kar suyi kasa a gwiwa wurin bayyana ma yan sanda baynai da zai taimaka wurin bincike
  • Yan sanda na cigaba da bin dazuzuka da kuma wuraren da ake gani maboya ne ga mahara

Mun kawo muku labarin rahoton yadda wasu mutane dauke da makamai suka kutsa cikin wata makaranta kimanin awanni 48 da suka wuce.

Malamai da dalibai na cikin wadanda aka sace yayin da aka hallaka wani dan sanda.

A wata sanarwa, DSP Nafiu Abubakar, Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Kebbi, Ya ce dole maharan zasu fuskanci doka.

Yace:

“Tawagar‘ yan sanda da ke Bakin aiki a yanzu haka suna ci gaba da bin ‘yan fashi wanda a ranar 17 ga Yuni, 2021 suka kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri, Jihar Kebbi.
Tawagar ta hada da ‘yan sanda daga rundunar Police Mobile Force, Masu yaki da satar mutane da kuma ta’addanci suna ci gaba da binciken dazuzzukan da ke kusa, hanyoyi da wuraren da ake zargin maboyan mugayen masu aikata laifi ne. ”

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Muna Zawarcin Yan Bindiga a Kebbi Ruwa a jallo - Yan Sanda
Muna Zawarcin Yan Bindiga a Kebbi Ruwa a jallo - Yan Sanda
Asali: Facebook

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Kwamishinan‘ yan sanda na jihar Kebbi, CP Adeleke Adeyinka yayin da yake Allah wadai da harin wanda yayi sanadiyar mutuwar dan sanda daya da kuma harbin bindiga kan daya daga cikin daliban, yana tabbatarwa iyaye da kuma masu kula da daliban cewa rundunar tana kokarin bin didigi wurin bin sawun maharan domin tabbatar da ceto daliban da malaman da suka bata.

Bayan kaddamar da harin, malamai uku tare da daliban da ba a san adadin su ba har yanzu ba a gansu ba.

A halin yanzu Kwamishinan‘ yan sanda na kira ga mazauna jihar ta Kebbi da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanai na gaggawa da za su taimaka wajen magance aikata irin wanan laifin da kuma cafke masu laifin.

Ya ba da tabbacin cewa rundunar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin cewa mutanen da aka sace sun dawo ga danginsu cikin aminci kuma an hukunta masu laifi.

An ceto wasu dalibai cikin wadanda aka sace

Malamai da daliban kwalejin gwamnatin tarayya dake Yawuri a jihar Kebbi, wadanda jami'an tsaro suka ceto daga hannun 'yan bindiga a sa'o'in farko na ranar Juma'a, a halin yanzu suna asibiti inda ake kula da lafiiyarsu.

Bayan aikin jami'an hadin guiwa na tsaro, malamai biyu da dalibai biyar sun kubuta yayin da wata daliba mace ta mutu a harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel