Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yayan Wani Manomi 2, Sun Sace Wasu Mutum 2 a Jihar Ondo

Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yayan Wani Manomi 2, Sun Sace Wasu Mutum 2 a Jihar Ondo

  • Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kutsa gidan wani manomi, sun kashe yayansa 2 tare da sace wasu 2
  • Rahoto ya nuna cewa Maharan sun shiga garin Ajowa Akoko da safe, inda suka yi ƙoƙarin sace wani sanannen mutum
  • Jami'an tsaron soji ne suka samu nasarar fatattakar yan bindiigan daga yankin

Wasu yan bindiga sun kutsa cikin gidan wani manomi mai suna, Dele, a yankin Ajowa Akoko, ƙaramar hukumar Akoko ta arewa, jihar Ondo, inda suka kashe ƴaƴansa 2, sannan suka sace wasu biyu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023

Yan bindigan sun shiga garin, suka nufi gidan wani sanannen mai kiwon shanu, Yinka Oludotun, da safe amma ba su samu nasarar isa gidan ba, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Yan bindiga sun kashe mutum 2 sun sace 2 a Ondo
Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yayan Wani Manomi 2, Sun Sace Wasu Mutum 2 a Jihar Ondo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa wasu gwarazan jami'an soji ne suka kawo ɗauki, inda suka kori yan bindigan daga yankin.

"Da yan bindigan suka fahinci ba zasu samu nasarar sace Yinka ba, sai suka kusta kai gidan Dele, suka kashe yayansa biyu kuma suka tafi da wasu biyu." inji majiyar.

KARANTA ANAN: Baba Oyoyo-Baba Oyoyo: Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari

Kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Yace a halin yanzun jami'an tsaro suna kan bincike, kuma za'a tabbatar an kuɓutar da waɗanda aka kama ba tare da cutarwa ba.

"Eh, mun samu rahoton kai hari Ajowa, kuma yanzun haka jami'an tsaro suna bibiyar maharan. Kuma ana cigaba da bincike," inji Ikoro.

A wani labarin kuma Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

Wani artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga ya laƙume rayukan yan sanda 4, da jami'in hukumar NCDC ɗaya.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel