Baba Oyoyo-Baba Oyoyo: Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari
- Mutanen Maiduguri sun tarbi shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, cikin murna da farin ciki
- Yayin da jirgin Buhari ya ɗira, babu sautin dake tashi daga bakin jama'a sai na Baba Oyoyo! Baba Oyoyo
- A halin yanzun shugaba Buhari ya jagoranci buɗe wasu ayyuka a makarantar saƙandire da kuma jami'ar jihar Borno
Sautin Baba Oyoyo! Baba Oyoyo, shine sautin da ya cigaba da tashi yayin da jirgin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauka a Maiduguri, jihar Borno, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri
Buhari ya kai ziyara jihar Borno ne domin ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamna Babagana Umaru Zulum ya kammala.
Jirgin shugaban ƙasa Buhari ya dira da misalin ƙarfe 9:30 na safe a filin sauka da tashin jirage dake Maiduguri, inda mutanen da suka zo tarbar shugaban suka nuna tsantsar farin cikin su.
Buhari Zai kai ziyara fadar mai martaba shehun Borno
Wata majiya dake kusa da shugaba Buhari, ta bayyana cewa shugaban zai ziyarci fadar mai martaba shehun Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa direbobi na fusakantar matsi da wahala yayin da aka kulle hanyoyin dake cikin birnin Maiduguri saboda zuwan shugaban.
KARANTA ANAN: Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya ƙaddamar da wasu ayyuka a makarantar sakandire
Shugaba Buhari ya jagoranci buɗe wasu sabbin ayyuka a makarantar sakandiren gwamnati dake Njimtilo, da kuma jami'ar jihar Borno.
Ɗaliban sakandiren sun tarbi shugaban Ƙasa Buhari, yayin da ya iso makarantar su domin buɗe ayyuka.
Hotunan ɗaliban da suka tarbi shugaba Buhari
A wani labarin kuma Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara
Wani artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga ya laƙume rayukan yan sanda 4, da jami'in hukumar NCDC ɗaya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Asali: Legit.ng