Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarkashin jam'iyyar HDP, Chief Ambrose Owuru, ya bukaci INEC ta dakatar da zaɓen 2023
  • Owuru ya buƙaci kotu da ƙwace mulki daga hannun Buhari ta bashi, sannan a rantsar da shi cikin gaggawa
  • A halin yanzun, kotu bata sanya ranar da zata fara sauraron wanna ƙarar ba

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar HDP a zaɓen da ya gabata, Chief Ambrose Owuru, ya garzaya kotu da bukatar a dakatar da hukumar INEC daga shirin gudanar da zaɓen 2023, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Baba Oyoyo-Baba Oyoyo: Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari

Owuru, wanda yana daga cikin mutum huɗu da duka ƙalubalanci nasarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen 2019, kuma yanzun ya sake buƙatar kotu ta dakatar da zaɓen 2023 gaba ɗaya.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya buƙaci a dakatar da shirin zaɓen 2023
Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daga cikin waɗanda ya shigar ƙara gaban kotu akwai shugaba Buhari, Antoni janar, da kuma hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.

Chief Ambrose Owuru ya buƙaci kotu ta kwace mulki a hannun Buhari ta bashi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Owuru, da jam'iyyarsa sun ƙalubalanci nasarar shugaba Buhari har gaban kotu.

A ƙarar da suka shigar, sun nemi kotu ta bayyana Chief Owuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen 2019, sannan a gaggauta rantsar da shi.

KARANTA ANAN: Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

Wani sashin karar yace: "Bayan rantsar da ni a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ya kamata kotu ta umarci shugaba Buhari ya maido da albashinsa da alawus ɗin da ya amsa tun sanda ya shiga ofis a 2019."

A halin yanzu, kotu ba ta sanya ranar da zata fara sauraron wannan ƙarar da aka shigar gabanta.

A wani labarin kuma Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya roƙi jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu bara gurbi suna kashe su, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yaje ta'aziyya ga hukumar a hedkwatar ta dake babban birnin jihar, Owerri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262