Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

  • Wani artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga ya laƙume rayukan yan sanda 4, da jami'in hukumar NCDC ɗaya
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin
  • Yace jami'ai sun samu nasarar kashe yan bindiga da yawan gaske, amma sun tafi da gawarwakin yan uwansu

Jami'an tsaro 5 sun rasa rayuwarsu a wata fafatawa da suka yi da wasu yan bindiga a ƙauyen Gora Namaye, ƙaramar hukumar Maradun, jihar Zamfara.

Jami'an tsaro na hukumar yan sanda guda 4 tare da jami'in hukumar NSCDC ɗaya ne suka rasa rayukan su a artabun da ya ɗauki tsawon awanni ana yi, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Wata majiya ta tabbatar wa jaridar dailytrust faruwar lamarin ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Dalla-Dalla: Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarabawar JAMB 'Mock' 2021

Jami'an tsaro sun kashe yan bindigan da dama a fafatawar

Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kashe yan bindiga da dama waɗanda suka tare Hanyar Gusau-Sokoto.

Shehu yace a halin yanzun an tsaftace hanyar, su kuma yan bindigan da suka yi ƙoƙarin fashi a kan hanyar an kore su.

Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara
Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yace: "Jami'an yan sandan jihar Zamfara sun samu nasarar fatattakar yan fashi da makami waɗanda suka tare babbar hanyar Sokoto-Gusau, kusa da Dogon Ƙarfe, ƙaramar hukumar Bakura."

"Maharan sun yi ƙoƙarin kwace dukiyoyin al'ummar yankin waɗanda ba su ji ba basu gani ba, sai-dai yan sanda sun samu nasarar korar su daga wajen."

KARANTA ANAN: Kasar Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Laifin da Ya Aikata Tun Yana Yaro

"An yi musayar wuta na tsawon awanni huɗu tsakanin jami'ai da kuma yan bindigan, inda sakamakon haka ne aka kashe yan ta'adda da dama, sauran suka tsere da raunin harbi a jikin su."

"Sun ɗauke gawarwakin yan uwan su da aka kashe sabida yawan da suke da shi, domin ana kiyasin sun kai aƙalla 200," inji shi.

A wani labarin kuma Babbar Magana, Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun yayi alƙawarin rushe duk wani gida da aka kama masu garkuwa na boyewa a cikinsa.

Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana zaman lafiya a jiharsa kuma su samu mafaka a cikinta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel