Soke Hajji: Hukumar Alhazai ta Kano ta kafa kwamitin mayar wa da maniyyata kudinsu

Soke Hajji: Hukumar Alhazai ta Kano ta kafa kwamitin mayar wa da maniyyata kudinsu

  • An bukaci maniyyatan da suke bukatar a mayar musu da kudadensu da su rubuta wa hukumar ta hanyar jami’an Hajjin a kananan hukumomi
  • Za a kafa kwamitin da zai kunshi wakilan jami’an tsaro da sauransu
  • Saudiyya ta soke gudanar da Hajjin bana sakamakon Covid-19

Sakamakon soke aikin Hajjin bana da hukumomin Saudiyya suka yi, hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta ce za ta kafa kwamitin mutum 11 domin mayar wa da maniyyatan da suka riga suka biya kudin aikin hajji.

Babban Sakataren hukumar, Muhammad Abba-Danbatta, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Laraba a birnin Kano.

Ya bayyana cewa kwamitin zai kunshi masu ruwa da tsaki daban daban ciki har da hukumar DSS da ICPC da sauran jami’an tsaro da ma ’yan jarida da dai sauran su.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Soke Hajji: Hukumar Alhazai ta Kano ta kafa kwamitin mayar wa da maniyyata kudinsu
Soke Hajji: Hukumar Alhazai ta Kano ta kafa kwamitin mayar wa da maniyyata kudinsu Hoto: Haramain
Asali: Twitter

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

A cewarsa,

“Za a mayar wa dukkanin maniyyatan kudadensu.
“Akwai wasu ayyukan da muke gudanarwa a hukumar alhazan a nan Kano kamar dakin sha-ka-tafi da otel.
‘’Dakin sha-ka-tafin mai dakuna 10 kusan kashi 99 na aikin ya kammala. An girke dukkanin na’urorin bincike tare da samar da ma’aikatan da za su yi aiki a wajen. Sannan otel din mai daukar mutum 500 da zai ci kudi miliyan N298 ya kai kusan matakin rabi.
“Maniyyatan da suke bukatar a mayar musu da kudadensu za su rubuta wa hukumar bukatar hakan ta hannun jami’an kananan hukumomin da suke."

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, a ranar Litinin din nan ta tabbatar da soke aikin Hajjin banan da hukumomin Saudiyyar suka yi saboda kariya daga cutar Covid-19.

NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.

Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja.

Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel