Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

  • Shugaban EFCC yace yaki da cin hanci yana neman ya fi karfinsa amma yana kokari
  • An sha yi wa Shugaban barazanar kashe shi
  • Yace Cin hanci da rashawa ya yi katutu a harkar bayar da kwangiloli

Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa yana yawan samun sakonnin barazanar kisa.

Shugaban ya bayyana hakan a wani shirin kafar telebijin na Channels mai suna Sunrise Daily ranar Talata da safe.

Da aka tambaye shi ko mene ne zai ce kan kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari yake yawan furtawa cewa “Cin hanci da rashawa na ramuwar gayya kan yaki da shi”, Shugaban ya ce ko a makon jiya yana birnin New York, na Amurka inda wani ya kira shi yana masa barazana.

A makon jiya ina a birnin New York lokacin da wani wani wanda ba a ma kan binciken sa ya kira wani babba a kasa.

“Matashin ya ce ‘Zan kashe shi (Shugaban EFCC), zan kashe shi’.

“Ina samun sakonnin barazanar kisa. Don haka da gaske ne cewa yaki da cin hanci yana ramuwar gayya,” inji shi.

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa
Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Da yake magana kan cin hanci a bangaren aikin gwamnati, ya ce akwai gibi sosai musamman ma a harkar samun kwangila, kamar “kwangilar yanzu-yanzu”.

Ya ce: “Wata hukumar gwamnati ta yi kaurin suna a hakan. Ta mayar da dukkan kwangilolinta a zaman na gaggawa.”

Koda yake, ya ce, hukumar tana da nata dabarbarun wajen gano nau’ukan cin hanci daban daban daya daga cikinsu shi ne “binciken yiwuwar cin hanci a kafofi da ma’aikatu ”.

Ya ce: “Na rubuta wa Ministan kuma nan ba da jimawa ba za mu fara binciken yiwuwar cin hanci a dukkanin ma’aikatu da kafofin gwamnati da ke karkashin Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur domin duba inda suke da nakasu sannan mu ba su shawarwarin abin da ya dace su yi.”

Da aka tambaye shi ko girman yaki da cin hancin da ake yi a Najeriya yana neman ya fi karfinsa, sai ya amsa da cewa “Eh kuma a’a.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel