Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

  • Wasu ma’aurata sun samu karuwa bayan shafe fiye da shekara 20 suna neman haihuwar.
  • Wata mata mai suna Faith Elvis Ovie, wacce take dangin ma’auratan ta nuna godiyarta ga Allah
  • ’Yan Najeriyar da suka yi tsokaci kan hotunan jariran ’yan biyu sun tura sakonnin taya murna da fatan alheri ga ma’auratan

Wadansu ma’aurata a Najeriya suna cike da murna da fara’a bayan sun samu karuwa na farko da ’yan biyu bayan shafe fiye da shekara 20 suna zaman jiran tsammani.

Wata dangin ma’auratan mai suna Faith Elvis Ovie ita ce ta sanar da labarin a shafin Facebook ranar 12 ga watan Yuni.

Ta ce jiran nasu ya haifar musu da samun ’yan biyu kuma mutane da dama sun taya su murnar samun alherin.

‘’Allah Ya ninninka musu alherinsa wajen ba su ’yan biyu namiji da mace.,’ Kamar yadda ta wallafa a shafin Facebook din.

Daya daga cikin hotunan da aka wallafa a facebook din ya nuna matar lokacin da take dauke da juna biyu, sannan dayan kuma ya nuna jariran ’yan biyu.

Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21
Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa Hoto: Faith Elvis
Asali: Facebook

A hirarta da kafar Legit, Elvis ta bayyana sunayen iyayen da cewa Justice Onadaipe da mai dakinsa Mary Onadaipe. Ta ce suna zama a Warri, cikin Jihar Delta.

Ta bayyana yadda suka samu labarin farin cikin inda ta ce mijin saboda murna ya fasa zuwa aiki, sannan ta tabbatar da cewa ma’auratan sun yi ta jiran samun haihuwar har tsawon shekara 21.

Wadansu ma’auratan ma sun yi murnar

Har wayau, kafar Legit tun da farko ta ruwaito wadansu ma’auratan a Najeriyar su ma daga karshe sun samu haihuwar ’yan biyu bayan zaman jira na shekara 27 ba tare da samun haihuwa.

Ma’auratan Dokta Mike da Dokta Modupe Obiora sun yi aure ne tun ranar 11 ga watan Disamban 1993, sun kasance suna ta yin addu’ar samun karuwa tun lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel