NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita

NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita

  • Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa ta tabbatar da soke aikin Hajji ga 'yan Najeriya a wannan shekarar
  • Hukumar ta ce maniyyata masu bukatar a mayar musu kudinsu za su iya karba ba tare da bata lokaci ba
  • Hakazalika, masu bukatar a adana kudadensu zuwa wata shekara, su jira hukumar ta fidda karin bayani

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.

Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.

KU KARANTA: Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

An tabbatar da cewa 'yan Najeriya ba za su je aikin hajjin bana ba
Maniyyata aikin a Najeriya yayin kokarin shiga jirgi domin zuwa kasar Saudiyya Hoto: bbci.co.uk
Asali: UGC

“Hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta samu labarin soke aikin Hajji ga mahajjatan kasa da kasa na kakar 2021.

“Mun yarda cewa Allah ne ya tsara cewa dinbin mutane ba za su yi aikin Hajjin ba a wannan shekarar.

Shugaban ya kuma yabawa maniyyata 'yan Najeriya bisa goyn baya da biyayya da suka nuna ga hukuncin da kasar ta Saudiyya ta yanke a bara, yana mai kira garesu da su yi hakuri a wannan shekarar ma, News Digest ta ruwaito.

Ya ce: "Duk da haka, amma ga wadanda har yanzu za su so aje kudadensu, hukumar ta bukaci su da su jira karin bayani da yanke shawara daga hukumar."

Hakazalika“Kamar yadda yake a shekarar da ta gabata, alhazan da suka nemi a mayar masu da kudin aikin hajjin za a ba su ba tare da bata lokaci ba."

KU KARANTA: Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa

A wani labarin, Shugaban Masallatai biyu mafi daraja a Saudiyya (Haramain Sharifain) Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya tube Daraktan da ke kula da limamai da ladanai a masallacin Manzon Allah dake birnin Madina.

An tube shi ne saboda samun jinkirin tayar da sallar Asuba bayan an kira Sallah na tsawon minti 45, kamar yadda Hukumomin da ke kula da Masallatan Makkah da Madina a Saudiyya, Haramain Sharifain suka sanar.

Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ce shugaban Masallatan Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya bukaci a samar da limamai biyu a ko wace Sallar farilla tare da ladanai uku masu jiran ko ta kwana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel