Wani manomi ya Sheke wani makiyayi har lahira saboda kiwo a gonarsa

Wani manomi ya Sheke wani makiyayi har lahira saboda kiwo a gonarsa

  • Manomi mai suna Adebayo ya harbe wani makiyayin Matashi har lahira
  • Wata kotun Magistrte da ke Ilorin ta ba da daman a cigaba da tsare mai laifi
  • Wanda ake Tuhuma bai ja dogon zare ba ya amsa laifinsa har ya so ya binne gawan

Wata kotun Magistrate dake Ilorin ta bada izinin a cigaba da tsare wani Manomi mai suna Segun Adebayo Wanda ya harbe wani Makiyayi har lahira a gidan kaso da ke Oke-Kura.

Hukumar yan sandan tana tuhuman Adebayo da laifin kisa.

Mai Sharia Ibrahim Dasuki wanda ya bada izinin haka, Ya dage Zaman sauraro har zuwa June 22 inda zaa cigaba da sauraron karan.

Tun da fari ne, Lauya mai suna Inspekta Zachaues Folorusho lauya Mai kare wanda aka kashe, Ya bayyana ma Kotu cewa Dan uwan Mamacin mai suna Muhammad Adamu ya kawo ma 'yan Sanda rahoton Cewa dan uwansa fa bai dawo daga kiwo ba.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Wani manomi ya Sheke wani makiyayi har lahira saboda kiwo a gonarsa
Wani manomi ya Sheke wani makiyayi har lahira saboda kiwo a gonarsa

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Dan Sanda ya bayyana Cewa wanda ake tuhuma wato Adebayo ya amsa laifin kisan da yayi, A dalilin ya kama Makiyayi yana kiwo a gonar sa.

Folorunsho ya kara bayyana cewa, Wanda ake tuhuma ya amsa laifin shi ya kashe wannan matashi mai Shekara Sha takwas, A inda yayi kokarin boye gawan.

Ya roki Alfarmar kotu data cigaba da tsare Mai laifin domin laifinsa ya fi karfin beli.

Haka zalika Jaridar pulse.ng, ta bayyana cewa wanda ake tuhuma bai yi musu ba ya amsa laifin sa.

Laifin gwamnonin PDP ne, fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ta zargi gwamnonin a karkashin jam’iyyar PDP, da kin goyon bayan kudirin kawo karshen rikicin makiyaya a kasar ta yadda za a ceci rayukan jama'a da dukiyoyinsu.

Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar a karshen mako a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel