Gwamnatin Buhari ta zargi gwamnonin PDP da kin kawo karshen rikicin makiyaya

Gwamnatin Buhari ta zargi gwamnonin PDP da kin kawo karshen rikicin makiyaya

  • Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana lafin gwamnonin PDP wajen kin magance rikicin makiyaya
  • Fdar shugaban kasa ta ce gwamnonin sun ki amincewa da tsarin da zai ba dukkan 'yan Najeriya 'yancinsu
  • Hakazalika, ta bayyana yadda kudurinta na samawa makiyaya matsuguni zai taimaka matuka a kasar

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ta zargi gwamnonin a karkashin jam’iyyar PDP, da kin goyon bayan kudirin kawo karshen rikicin makiyaya a kasar ta yadda za a ceci rayukan jama'a da dukiyoyinsu, BBC ta ruwaito.

Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar a karshen mako a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a ranar Litinin.

A martaninta cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya ce gwamnonin PDP ba su samar da mafita ga matsalolin kasar ba amma sun fi sha'awar abinda ya shafe su.

KU KARANTA: Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Wajen Tantance Shi

Fadar shugaban kasa ta koka kan kin da gwamnonin PDP suka yi na shirin makiyaya
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

“Wannan shirin na samar da matsuguni ga makiyaya ya kawo 'yanci da sauyi na zamani don kawo mafita ga kalubalen da al'ummomi daban-daban na kasarmu suka fuskanta.
"Amma gwamnonin PDP suka ki amincewa da shi, suka hana dukkan 'yan Najeriya 'yancinsu na tsarin mulki na rayuwa da aiki a kowace jiha ta Tarayya sun fifita yin kira ga rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan Najeriya''

KU KARANTA: Da Duminsa: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin Sojoji a Borno

Ghali Na’Abba Ya Bayyana Yadda Gwamnoni Suka Jefa Najeriya Cikin Matsaloli

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya caccaki gwamnoni a Najeriya yana mai cewa sun lalata dimokiradiyyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Na’Abba, yayin da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Talata, ya ce gwamnonin jihohi sun lalata dimokiradiyya, suna yin magudi a zabukan fidda gwani na jam’iyyunsu na siyasa don wanda suke so ya fito.

“Gwamnoni sun ja layi a siyasa wanda in kai ba yaronsu bane, ba za ka zama kowa ba ko kuma a zabe ka a dukkan matakai. Wannan yana faruwa a duka PDP da APC.

Rikicin Makiyaya da Manoma: Makiyaya Sun Sare Hannun Wani Manomi a Yayin Rikici

A wani labarin, Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.

Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.

An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.

Rahoton da Legit ta samo ya bayyana cewa manomin da abokansa sun fatattaki makiyayan. Sai dai, an ce daya daga cikin makiyayan ya zaro adda ya datse hannun manomin nan take.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Demokradiyya da misalin karfe 1 na rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel