'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama
- Yan bindiga sun kai hari unguwanin Kofar Gayan da Kofar Kona a karamar hukumar Zaria, jihar Kaduna sun sace mutane
- Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta bakin mai magana da yawunta ASP Mohammed Jalinge ta tabbatar da harin
- Wasu mazauna unguwannin da aka kai harin sun bada bayanai kan yadda yan bindigan suka kutsa gidajensu suka yi awon gaba da yan uwansu
Kwanaki biyu bayan harin da aka kai a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, Zaria, jihar Kaduna, yan bindiga sun sake kai hari unguwannin Kofar Gayan da Kofar Kona sun sace mutane da dama, a cewar yan sanda.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ASP Mohammed Jalinge, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, wanda ya tabbatar da hakan ya ce har yanzu yana kan tattara bayanai domin ya sanar da yan jarida.
DUBA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Rikici Ya Barke a Wurin Taron Jam'iyyar APC a Kano
Sai dai wani jami'in hukumar yan banga na jihar Kaduna, (KadVS) wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Lahadi a Zaria amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 12.01 zuwa 1.00 na daren Asabar.
Jami'in, wanda bai bayyana adadin mutanen da aka sace ba ya ce lamarin ya faru ne a kusa da Makaranatar Sakandare na Mata ta Gwamnati da ke Kofar Gayan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wani shaidan gani da ido, Abdullahi Mohammed, mazaunin yankin ya shaidawa NAN cewa a kalla mutane 12 ne yan bindigan suka sace yayin harin.
Ya kara da cewa kimanin mutane takwas yan gida daya ne yayin da sauran kuma daban-daban aka sace su.
KU KARANTA: Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Jam'iyyar APC Biyu a Makurdi
Kazalika, diyar daya daga cikin wanda abin ya shafa, Hafsat Kusfa, ta ce yan bindigan sun kutsa gidansu misalin karfe 12.01 na dare sannan suka fito da su suka jera su a kofar gida.
Ta kara da cewa yan bindigan da adadinsu ya kai bakwai dauke da bindigu da adduna sun tafi da mutane takwas yan gidansu ciki har da mahaifinta, mahaifiyarta da yan uwanta maza da mata.
Hafsat ta ce daga bisani an sako mahaifiyarta da mahaifinta da wasu wadanda aka sace sakamakon kokarin da jami'an tsaro suka yi na taka wa yan bindigan birki.
Kada a biya kudin fansa idan masu garkuwa sun sace ni, Mai dakin El-Rufai
A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.
Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.
Asali: Legit.ng