Sojojin Nigeria na buƙatar addu'a domin yin nasara kan Boko Haram, Janar na Sojoji

Sojojin Nigeria na buƙatar addu'a domin yin nasara kan Boko Haram, Janar na Sojoji

  • Janar a rundunar sojojin Nigeria, Birgediya Janar Abimbola Yussuph ya ce sojojin Nigeria na bukatar addu'o'i don nasara kan Boko Haram
  • Birgediya Janar Abimbola Yussuph ya yi wannan jawabin ne a wani coci a babban birnin tarayyar Abuja a ranar Lahadi
  • Janar Abimbola Yussuph ya ce a kowanne yaƙi akwai matakin da ake bukatar karfafa wa sojojin gwiwa da addu'o'i domin samun nasara

Wani janar ɗin sojojin Nigeria, Birgediya Janar Abimbola Yussuph, a ranar Lahadi ya nemi a riƙa yi wa sojoji addu'a sosai domin samun nasara kan ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram, rahoton Daily Trust.

Dakarun Sojojin Nigeria
Sojojin Nigeria. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kaduna: Bayan Harin Kwalejin Nuhu Bamalli, Ƴan Bindiga Sun Yi Yunƙurin Kai Hari Wata Makarantar Sakandare

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja yayin bikin cika shekaru uku na cocin 'Temple of Mercy Prophetic Ministry', ya ce yakin da aka yi da ƴan ta'addan ya kai wani mataki wanda akwai bukatar addu'o'i, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, "Ko a wurin yaƙi, muna bukatar addu'o'i domin mutumin da ke yaƙin nan ya yi imani da wani abu kuma akwai bukatar a bashi ƙwarin gwiwa kan duk abin da ya yi imani da shi domin ya cigaba da yaƙin.

"Don haka, zan ce akwai bukatar addu'o'i domin cigaba da yaƙi kuma na san da izinin Allah za mu ga ƙarshen wannan yaƙin domin a kowanne yaƙi akwai lokacin da mutane za su zo su zauna a teburi guda."

KU KARANTA: Kowa ya kare kansa daga 'Yan Bindiga: Matawalle ya faɗawa Zamfarawa

A bangaren sa, faston da ke jagorantar cocin, Akin Akinnigbabe, ya buƙaci shugabannin Nigeria su saka tsoron Allah a zuciyarsu.

'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama

A wani rahoton kun ji cewa Kwanaki biyu bayan harin da aka kai a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, Zaria, jihar Kaduna, yan bindiga sun sake kai hari unguwannin Kofar Gayan da Kofar Kona sun sace mutane da dama, a cewar yan sanda.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ASP Mohammed Jalinge, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, wanda ya tabbatar da hakan ya ce har yanzu yana kan tattara bayanai domin ya sanar da yan jarida. Jama'a suna kai da kawowa a Kofar Gayan, Zaria.

Sai dai wani jami'in hukumar yan banga na jihar Kaduna, (KadVS) wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Lahadi a Zaria amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 12.01 zuwa 1.00 na daren Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164