Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin KEEP

Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin KEEP

  • Gwamnan Bauchi ya ware kimanin bilyan biyu don tallafawa mata da matasa
  • An sa wa wannan shiri suna ' Shirin karfafa mutane da samar da aikin yi na Kaura'
  • Wannan ya biyo bayan kaddamar da sabon sansanin jin dadin alhazai da gwamnan ya kaddamar

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin gwamnatinsa na KEEP.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Legit ta samu daga Lawal Muazu Bauchi mai tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani.

Ya ce yayin bikin mika kayayyakin da suka hada da jari, motoci da babura, injin markade da sauransu wa al'umar kananan hukumomin Gamawa da Zaki, gwamnan yace gwamnatinsa ta ware kimanin naira biliyan daya da miliyan dari biyar don bada jari da horaswa kan sana'oin hannu a fadin jiha.

Yace gwamnatinsa ta tsara kaddamar da rabon a wannan rana da ake bikin ranar dimokradiyya a Najeriya don nuna muhimmancin da matasa ke da shi a fannin shugabanci.

DUBA NAN:Rashin tsaro ya ta’azzara, an sace yara 930 a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Neja

Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin KEEP.
Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin KEEP.
Asali: Original

DUBA NAN: Ku ajiye makamai, ku nemi yafiya da sasanci, Rundunar soji ga Boko Haram

A cewar Gwamna Bala, shirin bada jari na KEEP zai tallafawa gwamnati wajen yaki da zaman kashe wando tsakanin al'umma musamman mata da matasa kuma tuni gwamnatin ta dauki nauyin horas da matasa kimanin dubu biyu kan noma da sana'oin hannu.

Ya yabawa al'umar kananan hukumomi biyun kan goyon bayan gwamnatin sa wajen gina sabuwar jihar Bauchi inda yace shirin za'a fadada shi zuwa dukkanin kananan hukumomi ashirin dake fadin jiha.

Saura da suka yi jawabi yayin bikin sun hada da shugaban jam'iyyar PDP ta jiha Alhaji Hamza Koshe Akuyam, Uwargidan Gwamna Hajiya Aisha Bala Muhammad, Yan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar Gamawa da Zaki, Auwal Jatau da Madaki Gololo dukkanin su yabawa gwamnan suka yi kan shirin da suka bayyana da matakin inganta tattalin arziki da yaKi da talauci tsakanin al'uma.

A bangare guda, gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan jihar sunan me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar.

Da yake jawabi yayin bude sansanin, me alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya fara da yabawa Gwamna Bala Muhammad kan samar da sansanin da a cewar sa ya dace da zamani.

Sultan Sa'ad yace sanya sunan sa ga sansanin babban kalubale ne akan sa na tabbatar da anyi amfani da kula da shi yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel