Rashin tsaro ya ta’azzara, an sace yara 930 a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Neja
- ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga suna neman hana makarantun boko sakat a Najeriya
- Bincike ya nuna an sace yara fiye da 900 daga makarantu a cikin watanni shida
- Jihohin Kaduna, Katsina, da Neja suna cikin inda aka fi matsawa lamba a kasar
Yaran makarantar sakandare da na gaba da sakandare akalla 936 ake zargin cewa ‘yan bndiga sun yi garkuwa da su daga Disamban 2020 zuwa Yunin 2021.
Jaridar Punch ta yi wani bincike inda ta gano cewa miyagun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adan Boko Haram sun fi yin wannan ta’adi a jihohin yammacin Arewa.
Daga cikin wuraren da aka yi awon gaba da yaran makaranta akwai garin Kankara (Katsina), Mahuta (Katsina), Afaka (Kaduna), da kuma Kasarmi (Kaduna).
KU KARANTA: Sojoji sun bukaci Boko Haram su mika wuya, su huta
Sauran wuraren su ne; Kagara (Neja), Tegina (Neja), Jangebe (Zamfara), Effurun (Delta) da Ohordua (Edo).
Wasu daga cikin iyayen wadanda wannan abu ya shafa sun ce ba za su sake barin ‘ya ‘yansu su koma makaranta ba, saboda gudun ‘yan bindiga su sake sace su.
Alhaji Ibrahim Bageba, wanda ya na cikin wadanda aka sace wa yara a Jangebe, ya ce: “Na cire ‘ya ‘ya na daga makaranta saboda matsalar tsaro da ake fama da ita.”
Wata Baiwar Allah mai suna Hafsat Sani da aka dauke ‘ya ‘yanta biyu a makarantar Jangebe ta ce: “Iyaye da dama suna shakkar kokarin gwamnati wajen kare al’umma.”
KU KARANTA: Janar Abdussalami, Obasanjo, Sarkin Musulmi sun yi zama kan batun tsaro
“An sace mani yara biyu a harin da aka kai, ba zan bari su koma karatu ba sai an yi wani abu.”
Darektan yada labarai na ma’aikatar ilmi na tarayya, Bem Goong, ya shaida wa jaridar Punch irin kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na tsare makarantun kasar.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a na su bangaren, wasu gwamnonin jihohi sun dauki matakin rufe duk makarantun kwana har sai lokacin da aka samu zaman lafiya.
A karshen makon da ya gabata ne aka ji Miyagun ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata da Yara, sannan sun harbe Dalibai bayan sun shiga Nuhu Bamalli Poly da ke Zaria.
Bayan an rasa rai da aka dura wannan makaranta da ke hanyar zuwa Kaduna, ‘Yan bindiga sun yi sanadiyyar garkuwa da wasu mutum takwas, daga ciki da malamai biyu.
Asali: Legit.ng