Ku ajiye makamai, ku nemi yafiya da sasanci, Rundunar soji ga Boko Haram
- Rundunar sojin kasan Najeriya ta bukaci 'yan Boko Haram da su mika wuya tare da neman sasanci da yafiya
- AA Eyitayo, babban kwamandan Div 7 ne yayi wannan kiran a Maiduguri yayin taron manema labarai
- Shugaban rundunar Operation Hadin Kai yace 'yan ta'addan na cikin rashin natsuwa sakamakon luguden da ake musu
Rundunar sojin Najeriya tayi kira ga 'yan ta'addan Boko Haram da su ajiye makamai kuma su nemi yafiya tare da sasanci.
AA Eyitayo, babban kwamandan Div 7 na rundunar sojin kasa, yayi wannan kiran a ranar Lahadi a wani taro da rundunar ta shiryawa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Eyitayo ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna cikin dimuwa bayan gagarumin luguden wuta tare da matsanta musu da sojoji suka yi, TheCable ta ruwaito.
KU KARANTA: 'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari
KU KARANTA: Buhari: 'Yan Najeriya akwai mantuwa, har wadanda ake zargi da rashawa cin zabe suke
Yayi kira ga 'yan ta'addan da su mika wuya tare da amfani da wannan dama wurin tuba ko za su samu damar komawa rayuwarsu mai kyau, Crimefacts ta tabbatar.
Birgediya janar din wanda shine kwamandan sashi na daya na rundunar Operation Hadin Kai, yayi kira ga masu yada labarai da su wayar da kan 'yan ta'addan wurin kira garesu da su tuba.
"Ba mu zo nan don mu yi ta zubda jini ba, babu wanda ke farin cikin mutuwar jama'a," GOC yace.
"Wasu daga cikin 'yan ta'addan na sauraron kafafen yada labarai don haka yana da kyau mu yi musu magana da su bar tashin hankali, su mika wuya tare da neman yafiya da kuma sasanci."
A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya, ta yi amfani da jirginta na Alpha inda ta ragargaji wuraren garin Genu dake jihar Neja, lamarin da ya kawo mutuwar wasu 'yan bindiga tare da tserewar wasu.
PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin shanun satan da 'yan bindigan suka sato daga sansanin sojoji a jihar Katsina duk sun mutu.
Daya daga cikin bama-baman ya fada wurin liyafar biki a wani kauye dake da kusanci da garin, kamar yadda ganau suka tabbatar.
Asali: Legit.ng