Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazai sunan Sarkin Musulmi

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazai sunan Sarkin Musulmi

- An karrama Sarkin Musulmi a garin Bauchi ranar Litinin

- Gwamnatin jihar ta kaddamar da sabon sansanin maniyyata aikin hajji

- Kasar Saudiyya ta sanar da cewa mutum 60,000 kacal zasu yi hajji bana

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan jihar sunan me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar.

Da yake jawabi yayin bude sansanin, me alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya fara da yabawa Gwamna Bala Muhammad kan samar da sansanin da a cewar sa ya dace da zamani.

Wannan na kunshe cikin jawabin da hadimin gwamnan Bauchi na kafafen yada labaran zamani, Lawal Muazu Bauchi ya saki.

Sultan Sa'ad yace sanya sunan sa ga sansanin babban kalubale ne akan sa na tabbatar da anyi amfani da kula da shi yadda ya kamata.

Sarkin Musulmi Sa'ad yayi kira ga Gwamna Bala Muhammad da kada yayi kasa a guiwa wajen cigaba da samar da ayyukan raya jihar Bauchi.

KU KARANTA: Buhari Ya Naɗa Wa Mai Ɗakinsa, Aisha, Sabbin Hadimai Biyu

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan sunan Sarkin Musulmi
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan sunan Sarkin Musulmi Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

DUBA NAN: Dr. Isa Ali Pantami ya doke Takwarorinsa, ya lashe kyautar gwarzon Ministan 2020

A nasa tsokacin, Gwamna Bala Muhammad yace sansanin ya kunshi ofisoshin jami'an hukumar kula da jin dadin alhazai, asibiti, masallaci, kasuwar zamani da wuraren kwanan maniyata.

Yace gina sansanin ya biyo bayan kalubale da wahalhalu da maniyyata ke fuskanta a tsohon sansanin na wucin-gadi dake Games Village inda ya kara da cewa gwamnatinsa zata tabbatar da an kula tare da aiki da shi ta hanyoyin da suka dace.

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan sunan Sarkin Musulmi
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanyawa sabon sansanin alhazan sunan Sarkin Musulmi Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

Shima a nasa jawabin shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Kasa NAHCON, wanda ya samu wakilcin jami'in sanya ido na hukumar Magaji Hardawa yace sabon sansanin shine irinsa na farko a nahiyar Afrika.

Saura da suka yi jawabi yayin taron da suka hada da kakakin majalisar dokoki ta jiha Hon Abubakar Suleiman yabawa gwamnan suka yi kan aikin tare da alkawarin marawa gwamnatin baya wajen kula da sansanin.

A bangare guda, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya halarci taron kwanaki biyu kan jin bahasin al'ummar Najeriya kan garambawul wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da majalisar dattawa ta shirya.

Da yake bude taron da ya gudana a dakin taro na masaukin baki na soji dake fadar jihar, Gwamna Bala ya yabawa matakin majalisa ta tara kan garambawul wa kundin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel