Manjo Hamza Al-Mustapha Ya Ba Shugaban Hafsan Soji Shawari Kan Yaki da Boko Haram

Manjo Hamza Al-Mustapha Ya Ba Shugaban Hafsan Soji Shawari Kan Yaki da Boko Haram

  • Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) ya shawarci shugaban hafsan soji kan yadda zai yaki Boko Haram
  • - Al-Mustapha ya bayyana bukatar a yaki Boko Haram cikin gaggawa don samun zaman lafiya a fadin Najeriya
  • Ya bayyana haka ne a yau Lahadi, makwanni kadan bayan nada sabon shugaban na hafsan soji

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya shawarci Manjo Janar Faruk Yahaya, sabon shugaban hafsan soja (COAS) da ya kawo karshen rikicin Boko Haram a cikin mafi kankanin lokaci.

Al-Mustapha, wanda tsohon babban jami'in tsaro ne ga marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Lahadi, jaridar Today ta ruwaito.

Ya ce dole ne sabon hafsan sojojin ya tabbatar da hanzari wajen kawo karshen tayar da kayar baya wanda ya haifar da mummunar asara ta rayuka da dukiyoyi a sassan kasar.

KU KARANTA: NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita

Manjo Hamza Al-Mustapha ya shawarci sabon shugaban hafsan soja kan yaki da ta'addanci
Tsohon Jami'in Tsaron Shugaban Mulkin Soja Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Jinkirta yaki da Boko Haram zai zama babbar illa ga Najeriya. Hanzarta murkushesu shine mafi kyau.

“Hanzari yana da matukar mahimmanci, saboda bawai muna yaki ne da aka saba ba, ana bukatar hanzari saboda ya kamata Najeriya ta farfado daga wannan yanayin cikin sauri kamar yadda ya kamata.

"Na san wannan abu ne mai yiyuwa saboda na yi wasu aikace-aikacen gida," in ji Al-Mustapha yayin da yake taya Janar Faruk murna tare da yi masa addu'ar fatan alheri.

Al Mustapha ya kuma shawarci sabon hafsan sojojin da ya yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da nasara a yakin.

“Shawarata ita ce kada sojoji su kasance su kadai domin ba lamari ne na soja shi kadai ba.

“Boko Haram ta shafe sama da shekaru 20 a iya sani na, wato tun daga daukar cikinta har zuwa girmanta.

“Idan kana son shawo kan tayar da kayar baya, duk wani bayanin ayyukansu ya kamata ya kasance a tafin hannunka, a lokacin ne za ka iya cewa ina kan makuran halin da ake ciki.

"Dole ne ka samo hanyoyinsu na samun kayan aiki, tallafi da lantarki da kuma karfinsu, abinda suke yi a kullum da kuma yadda suke samun bayanai da sauransu," in ji shi.

Al-Mustapha ya ce dole ne hafsan sojan ya gano hanyoyin shigo da makamai zuwa cikin Najeriya sakamakon yaduwar makamai.

Al-Mustapha ya shawarci shugaban na hafsan soji ne makwanni kadan bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin mai maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, BBC ta ruwaito.

KU KARANTA: Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni

A wani labarin, An harbi wani soja da ke aiki a Birged ta 14 na Sojojin Najeriya a Ohafia a ranar Asabar yayin artabu tsakanin sojoji da wasu ‘yan ta'adda da ake zargin mambobin kungiyar tsaro ta Gabas ce ta ESN, Punch ta ruwaito.

An gano cewa rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan ta'addan suka kai hari sanannen tashan mota na Ebem a karamar hukumar Ohafia da ke jihar suka yi ta harbi ba ji ba gani.

Harbe-harben ya sa sojoji suka kawo dauki daga Hedikwatar Soja, a Ohafia, wadanda suka yi musayar wuta da mambobin kungiyar ta ESN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.