An Yi Artabu Tsakanin Sojoji Da ’Yan Ta’addan ESN, an Harbi Jami’in Soja

An Yi Artabu Tsakanin Sojoji Da ’Yan Ta’addan ESN, an Harbi Jami’in Soja

  • An yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga dake zargin 'yan kungiyar ESN ne a wani yankin jihar Abia
  • An ruwaito cewa wani soja ya mutu a yayin artabun wanda tuni aka zarce dashi asibiti don masa magani
  • Rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce ba ta samu labarin faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton

An harbi wani soja da ke aiki a Birged ta 14 na Sojojin Najeriya a Ohafia a ranar Asabar yayin artabu tsakanin sojoji da wasu ‘yan ta'adda da ake zargin mambobin kungiyar tsaro ta Gabas ce ta ESN, Punch ta ruwaito.

An gano cewa rikicin ya fara ne lokacin da ‘yan ta'addan suka kai hari sanannen tashan mota na Ebem a karamar hukumar Ohafia da ke jihar suka yi ta harbi ba ji ba gani.

Harbe-harben ya sa sojoji suka kawo dauki daga Hedikwatar Soja, a Ohafia, wadanda suka yi musayar wuta da mambobin kungiyar ta ESN.

KU KARANTA: Ba alluran Korona ke damuna na, sanya takunkumin fuska ke damuna, Shugaba Buhari

An kashe sojan Najeriya yayin artabu tsakanin ESN da sojoji
Wasu daga cikin 'yan bindigan ESN kenan dauke da makamai Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An samu labarin cewa an dauki sojan da ya ji rauni zuwa cibiyar lafiya ta tarayya da ke Umuahia domin yi masa magani.

Majiya ta ce “Mun samu labarin cewa wasu yara maza da ake zaton mambobin kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) ne suka kai sananne a tashar mota ta Ebem suka fara harbi sannan daga baya suka tsere," Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP Geoffrey Ogbonna bai iya tabbatar da rahoton faruwar lamarin ba.

Yankin kudu maso gabashin Najeriya na ci gaba da fuskantar da hare-hare daga 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar ESN ne.

KU KARANTA: Makiyaya basa rike AK-47, sanduna da adduna kadai suke rikewa, in ji Buhari

A wani labarin, 'Yan sanda a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da hada wa 'yan bingiyar IPOB layu da guraye, BBC ta ruwaito.

Uzoamaka Ugoanyanwu mai shekara 40 yana hada wa mayakan ESN layu, wato bangaren soja na kungiyar IPOB mai fafutikar ballewa daga Najeriya, a cewar Kwamishinan 'yan Sandan Imo Abutu Yaro.

An kame 'yan bindigan da suka kai hari gidan gwamnan jihar Imo tare da dakile tare a ofishin 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel