Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni

Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin Najeriya su dauki mataki kan ta'addanci

- Ya ce kada su tsaya jiran sai ya zo ya dauki mataki kan abubuwan da ke faruwa a fadin jihohinsu

- Shugaban ya yi martani ga gwamnonin da ke koka wa kan yawaitar hare-hare dake addabar yankunansu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.

Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.

Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.

KU KARANTA: Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni
Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Amma Buhari a wata hira da Arise TV a ranar Alhamis, ya bayyana wasu gwamnonin Kudu maso Yamma biyu da suka ziyarce shi kwanan nan don yin korafi game da cin amanar da makiyaya suka yi wa filayen gonakin jihohinsu.

Da yake bayyana hakan a matsayin barazana ga wadatar abinci, Buhari ya ce:

“Kun san wadannan mutanen fiye da ni, kuma an zabe ku ne ta hanyar dimokiradiyya don kare mutanenku. Kada ku zauna zaman jira na ni zan yi komai, ku dauki mataki."

KU KARANTA: Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk nadin da yake yi ya dogara ne da cancanta ba wai kabilanci ko yanki ba.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ganawa da gidan talabijin na Arise TV. An soki shugaban kasar kan zargin nada wasu karin ‘yan arewa a manyan mukamai.

A cikin hirar, shugaban na Najeriya ya ce ba zai iya sanya daidaito fiye da cancanta a nade-nadensa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel