Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara

  • Yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da harin da aka kai a karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara
  • Lokacin da labarin harin ya zo mana munyi gaggawar aika jami'an tsaro zuwa yankin, cewar hukumar
  • Wasu shaidu sun bayyana cewa maharan sun far ma kauyen ne cikin dare inda sukayi kan mai uwa da wabi

Hukumar Yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da harin da aka kai a karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara, inda akayi asarar rayukan mutum Casa'in

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, SP Shehu Mohammed, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gusau ranar Juma’a.

"Tabbas, zan iya tabbatar muku da cewa an kai wani hari a kauyen Kadawa da ke karamar hukumar Zurmi inda 'yan ta'adda suka bi dare wajen kai hari kan mutanen da ba'a sani ba suka kashe su cikin ruwan sanyi, ” Inji Mohammed.

“Da samun labarin harin, Kwamishinan‘ yan sanda, CP Hussain Rabiu, ya umarci hadin gwiwar jami’an tsaro da su dunguma zuwa yankin, domin su dawo da zaman lafiya da kwarin gwiwa a tsakanin al’ummomin tare da bin diddigin wadanda suka aikata laifin domin hukunta su.

“Kwamishinan, tare da shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Magarya, sun je wurin da abin ya shafa don yi wa iyalai ta’aziyya,” in ji shi.

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara
Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

NAN ta tattaro Bayanai daga wasu shaidun gani da ido da ke kauyen cewa ‘yan fashin sun mamaye kauyen da tsakar ranar Alhamis, suna magana cikin harshen da bama fahimta tare da harbin duk wani wanda ke kokarin tserewa annobar.

Daya daga cikinsu wanda ya bayyana sunansa Lawali ya ce an gano gawarwaki 67 a cikin kauyen yayin da aka tsince wasu 26 a wurare daban-daban da ke gefen kauyen tare da jikkata wasu da dama.

A bangare guda, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce kalubalen rashin tsaro a jihar na kara ta'azzara.

A wani furuci na gwamnan a ranar Asabar, Matawalle ya ce 'yan ta'adda sun koma yadda suke a da kafin zuwan gwamnatinsa - duk da kokarinta na rage yawaitar ta'addanci.

Ya koka kan yadda lamurran ta'addanci ke ci gaba da ta'azzara tare da bayyana yadda rashin tausayin 'yan ta'addan ke damunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel