A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

  • An bukaci a kyale ’yan kabilar Ibo su fice daga Najeriya salun-alun
  • Kungiyar ta bukaci a dakatar da yi wa tsarin mulkin 1999 gyaran fuska
  • A kira Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi domin taimaka wa Ibon su yi zabin zama ko ficewa.

Gamayyar kungiyoyin Arewa sun bukaci Majalisar Tarayya da ta ayyana dokar wajibci ta hanyar shirya kuri’ar raba gardama domin bai wa al’ummar yankin Kudu maso Gabas damar kada kuri’ar ko dai su ci gaba da zama a Najeriya ko akasin haka.

Gamayyar ta kuma bukaci Majalisar tarayyar da ta gayyato Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da kungiyar ECOWAS da su shigo domin fara batun bai wa ’yan kabilar Ibon damar zabin kansu.

Ta kuma bukaci ’yan majalisar ataryyar da su dakatar da aikin yi wa tsarin mulkin 1999 kwaskwarima, wanda suka bayyana aikin da wanda ake yin sa a lokacin da bai dace ba lura da yadda ake tayar da jijiyar wuyan neman ballewa.

Gamayyar ta bakin kakakinta, Abdul-Azeez Suleiman, ta fitar da matsayar ce a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja, rahoton Sahara Reporters.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi Read more: https://hausa.legit.ng/1420238-gwamnan-jihar-zamfara-bello-matawalle-ya-dakatar-da-sarkin-zurmi.html

A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa
A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa
Asali: Facebook

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

A cewar Shugaban gamayyar:

“Muna bukatar da a yi gaggawan dakatar da batun yi wa tsarin mulkin 1999 garambawul da ake gudanarwa yanzu haka domin mayar da hankali kan muhimmin abin da a yanzu yake damun kasar inda ’yan kabilara Ibo a karo na suke daukar makamai suna yakar Najeriya wanda hakan ya nuna babu wata fatar mu ci gaba da zama da su a cin kasa guda.
“Muna kuma kira ga Majalisar Tarayyar da ta matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba kan lallai ta gayyato Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da kungiyar ECOWAS domin su shigo su shirya hanyoyin da za a bi a bai wa ’yan kabilar Ibon damar yi wa kansu zabin da zai fisshe su bisa tanadin yarjeniyoyin kasa da kasa.

Ya kara da cewa a yau kowa yana shaida ayyukan assha da kungiyar IPOB ke yi da samun goyon bayan galibin shugabannin yankin na siyasa da na gargajiya da ’yan kasuwa da ma akasarin talakawan yankin inda hakan ke yi wa kasar illar gaske, riwayar Arise News.

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu ya bayyana yadda 'Yan Najeriya ke yaba masa a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan talabijin na Kasa NTA a ranar Juma’a.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin kasar ta ci gaba da kasancewa kasa dunkulalliya tare da samar da abubuwan yau da kullun na rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel