Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

  • Tun bayan zaman sa Shugaban Kasa a 2015, ya ciwo bashin tiriliyan N21 daga hukumomin lamuni
  • Bashin Najeriya ya karu da tiriliyan N33.1 cikin shekara biyar da suka gabata
  • A kowane wayewar garin Allah cikin shekara biyar da suka wuce, Najeriya ta rika cin bashin biliyan N10

Kowane dan Najeriya ana bin sa bashin fiye da N160,000 sakamakon basukan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rika karba tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2015.

Shugaban ya ranto bashin da yawansa ya kai tiriliyan N21 ttun watan Yulin 2015, da hakan ya sanya bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan N33.1 ya zuwa watan Maris din bana, kamar yadda bayanai daga Ofishin Kula da Basukan Najeriya (DMO) suka nunar.

Bayanan basukan da gwamnatin Shugaba Buhari ta karbo idan aka fasalta shi a ko wane wayewar garin Allah Ta’ala, kasar ta rika cin bashin fiye da biliyan N10 cikin shekara shida da suka gabata.

Hakan ya nuna cewa a cikin wadannan shekarun bashin da ke kan Najeriya a kowane wata ya rika karuwa da biliyan N309 wanda gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta ciwo.

Idan kuma aka rarraba basukan kan ’yan Najeriya, to ko wane dan kasar ana bin sa bashin fiye da N160,000.

Idan har za a biya wannan bashin, to sai Shugaba Buhari ya yi amfani da kashi 46.9% na kudaden shigar da kasar ke samu wajen biyan basukan. Hakan na nufin ke nan daga cikin tiriliyan N6.6, gwamnatin kasar za ta kashe tiriliyan N3.1 wajen biyan basukan da ke kanta a shekarar 2021.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa
Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU DUBA: Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

A daya gefen kuma kafar Legit a kwanakin baya ta ruwaito cewa Najeriya za ta kirkiro kudadenta na intanet wata biyar bayan da babban bankin kasar ya rufe asusun masu hada-hadar kudaden intanet din.

A cewar babban bankin, kafin nan da karshen shekarar nan Najeriya za ta kirkiro da nata kudin intanet din da zai yi gogayya da kudin intanet mafi tsada na bitcoin da ethereum da ma sauran makamantansu.

Babban bankin ya ce za a dauki kwararru da masu ruwa da tsaki a harkar kudin intanet din domin shigar da su kwamitin da zai kirkiro da tsarin kudaden na intanet.

Asali: Legit.ng

Online view pixel