Duk da Kokarina, Ta’addanci Ya Dawo Zamfara Kamar Da, Gwamna Matawalle
- Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana halin da jiharsa ke ciki na yawaitar aikata muggan laifuka
- Gwamnan ya koka kan ta'azzara da ta'addanci ke yi a fadin jihar cikin makwannin da suka gabata
- Ya bukaci jama'ar jiharsa da su kare kansu daga 'yan ta'adda duk lokacin da aka kai musu hari
Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce kalubalen rashin tsaro a jihar na kara ta'azzara, TheCable ta ruwaito.
A wani furuci na gwamnan a ranar Asabar, Matawalle ya ce 'yan ta'adda sun koma yadda suke a da kafin zuwan gwamnatinsa - duk da kokarinta na rage yawaitar ta'addanci.
Ya koka kan yadda lamurran ta'addanci ke ci gaba da ta'azzara tare da bayyana yadda rashin tausayin 'yan ta'addan ke damunsa.
KU KARANTA: Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa
A kalamansa, gwamna ya ce:
"A cikin makonnin da suka gabata, aikita ta'addanci ya sake komawa kamar yadda yake a da kafin zuwan gwamnatina."
“Mahara suna kashe mutane ba tare da la’akari da hankali ba. Mata, tsofaffi, da yara ba su tsira ba.
“A sakamakon haka, mutane da dama sun rasa muhallansu a kusan kowane gari a jihar.
“Ku shaidu ne a kan abin da muka cimma tun daga farkon gwamnatinmu, musamman kokarin samar da zaman lafiya da sulhu da muka fara kuma muka cimma.
Gwamnan ya kuma bukaci al'ummomi su kare kansu daga 'yan ta'adda yayin da ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da tsaro a jihar, in ji Channels Tv.
Yace:
"Ina tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da jajircewa a kokarin da muke yi na kawar da ta'addanci da dukkan nau'ikan aikata laifuka daga Jiha."
“A wannan yakin, babu wani da zai tsira. Duk wanda ke da hannu cikin wadannan ayyukan barna, komai girman matsayinsa, za a yi masa hukunci daidai da doka."
KU KARANTA: NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.
Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.
Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.
Asali: Legit.ng